Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce kasashen Musulmi za su yi duk abin da ya kamata don kare "alamar Musulunci" wato Masallacin Ƙudus, daya daga cikin wurare mafi tsarki ga Musulmai.
"Al'ummar Musulmi za su yi duk abin da ya kamata don kiyaye alamar Musulunci na Masallaci Mai Tsarki da ruhi iri daya," in ji Fidan a ranar Talata yayin jawabinsa a Taron Majalisar Ministocin Harkokin Wajen Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa karo na 162.
"Za mu ci gaba da ayyukanmu na hadin gwiwa don matsa wa kasashen duniya lamba kan su yi watsi da ayyukan Isra'ila."
Haram al Sharif kuma ana kiransa da Masallacin Ƙudus, wanda ya fuskanci kutse sosai daga shugabannin masu tsattsauran ra'ayi na Isra'ila a cikin 'yan watannin nan.
Fidan ya gargadi masu goyon bayan firaministan Isra'ila Netanyahu, yana mai cewa su ne ke da hannu wajen kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa a Gaza.
"Haka kuma za a yi musu hukunci."
A ranar Litinin, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kuma bukaci shugabannin Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmi ta OIC da su hadu a matakin jagoranci "ba tare da bata lokaci ba" don taimakawa wajen kare Birnin Kudus daga hare-haren Isra'ila.
Ƙarfafa dangantaka
Dangantakar Turkiyya da Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Larabawa ta samu ci gaba sosai tun lokacin da aka kafa ta a hukumance a shekara ta 2003, wanda ke da muhimman abubuwa da dama.
Wani muhimmin lokaci ya faru a watan Oktoban 2023 lokacin da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya ziyarci birnin Alkahira inda ya gana da Sakatare Janar na Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Larabawa, inda ya sake jaddada aniyar Turkiyya ta karfafa alaka da kasashen Larabawa.
An ci gaba da tattaunawa a watan Fabrairun 2024 a Ankara, inda mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Ahmet Yildiz ya gana da mataimakin babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ambasada Hossam Zaki, wanda shi ma ya halarci taron diflomasiyya na Antalya.
An fara gudanar da alaƙar ne da yarjejeniyar fahimtar juna a shekara ta 2004, kuma an ci gaba da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Larabawa a shekarar 2007.
A cikin wata fitacciyar huldar da aka yi, firaministan kasar na wancan lokaci kuma shugaban kasar na yanzu Recep Tayyip Erdogan ya yi jawabi a taron bude taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a shekarar 2011, inda ya bayyana irin kwarin gwiwar da Turkiyya ke da shi kan harkokin diflomasiyya na kasashen Larabawa da kuma karfafa dankon zumunci tsakanin Turkiyya da kungiyar kasashen Larabawa.