Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki matakin Isra'ila na ƙin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu, ya kuma yi gargadin cewa matsalar Falasdinu da ba a warware ta ba na barazana ga zaman lafiyar yankin baki daya.
Fidan ya bayyana a ranar Alhamis yayin wani taron ministoci kan Gaza a gefen Babban Taron MDD a birnin New York, wanda ƙungiyoyi Hadin Kan Ƙasashen Musulmi ta OIC da na Hadin Kan Ƙasashen Larabawa da ta Tuntuba ta Gaza da Tarayyar Turai da kuma Norway suka shirya, inda ya ce: "Ba za mu jira fatan alherin Isra'ila don aiwatar da shawarwarin samar da kasashe biyu masu cin gasin kansu ba."
Ya ce matakin da majalisar dokokin Isra'ila ta ɗauka na ƙin amincewa da kafa kasar Falasdinu da samar da kasashe biyu a fili yake.
"Wannan haɗama ce tsantsa wadda bai kamata a amince da ita ba."
Fidan ta bayyana cewa kisan gilla da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza na ci gaba da wanzuwa ba tare da an kawo karshensa ba, Fidan ya ce tattaunawar tsagaita wuta ta yi tsami ne saboda (Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu) yana yi musu ƙafar ungulu a duk lokacin da ake ganin an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta."
Ya ce Isra'ila ta fara faɗaɗa hare-harenta zuwa Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Birnin Ƙudus, yanzu kuma ta kai kasar Lebanon.
Kasashen duniya sun yi gargadi kan hare-haren da ake kai wa kasar Labanon, yayin da ake yaɗa yaƙin Gaza a yankin.
'Yankinmu na ci da wuta saboda Netanyahu'
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya ce, ƙasarsa ta daɗe tana bayyana cewa idan har ba a warware batun Falasdinawa ba, to hakan zai jefa ɗaukacin yankin cikin "baƙin rami."
"Haka ne abin da ke faruwa a Lebanon a yanzu haka, yankinmu na ci da wuta saboda Netanyahu," in ji Fidan.
"Muna cikin wani lokaci na ko-ta-kwana. Ta'addancin kisan kiyashin da Isra'ila ke yi ya ƙara wayar da kan jama'a game da gaskiyar lamarin," in ji shi.
Ya kuma tunatar da cewa, a baya-bayan nan wasu kasashe tara sun amince da kasar Falasdinu, inda ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa sauran kasashen ma za su bi sahun.
Fidan ta ce "Kasar Falasdinu an lalata. Gaskiya ne abokaina, ya kamata mu rungumi wannan a cikin labarinmu da kuma ayyukanmu," in ji Fidan.
Fidan ya ce ra'ayin ba da shawara na kotun kasa da kasa da kuma kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai kwanan wata 10 ga Mayun 2024, ya bude wata sabuwar hanya tare da kara da cewa: "Yanzu, mun kasance abu ɗaya ne ba mu kai ga samu ba a kan manufarmu."
"Ya kamata kasar Falasdinu ta zama cikakkiyar mamba ta Majalisar Dinkin Duniya," ya jaddada.
Ministan ya kuma ce mamayar da Falasdinu ke yi ba ta taɓa samar da zaman lafiya ko ƙarin tsaro a Isra'ila ba, yana mai cewa "aiwatar da tsarin samar da kasashe biyu zai kuma tabbatar da tsaro mai ɗorewa ga kowa.
Fidan ya kuma tunatar da cewa, Turkiyya ta ba da shawarar kafa wata hanyar tabbatar da tsaro don magance bukatun tsaron kasashen biyu.
Ya kara da cewa "Batun kasashe biyu karshen magana ne, kuma ya kamata a aiwatar da shi tun kafin lokaci ya ƙure."