Duk da tsokanar da Isra'ila ke ci gaba da yi, ana ci gaba da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas, in ji shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
Erdogan ya bayyana haka ne bayan taron majalisar ministocin ƙasar a ranar Litinin, inda ya jaddada shirin Turkiyya na ''yin dukkan mai yiwu wa don tabbatar da ɗorewar yarjejeniyar tsaigaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu.''
"Bambancin da ke tsakanin yanayin fursunonin Hamas da Isra'ila ta sako da kuma na Isra'ila da Hamas ta sako, sun bayyana ƙarara uƙubar ko wanne ɓangare,'' in ji shi, yana mai kwatance da yanayin lafiyar fursunonin da aka yi musayarsu a yarjejeniyar da aka cim ma.
''Ba za mu iya bar 'yan' uwanmu da ke Gaza su ƙadai a wannan lokacin ba. Ina sake jaddada kirana na bayar da tallafi ga al'ummar Gaza da ake zalunta gabanin watan Ramadan,'' in ji Erdogan.
Sake gina Turkiyya bayan girgizar ƙasa
Yayin da ake shirin tunkarar ranar tuni da iftila'in girgizar ƙasa da ta afku a Turkiyya a ranar 6 ga Fabrairun 2023, Shugaba Ergogan ya nanata ƙudurin ƙasar na sake gina yankunan da lamarin ya shafa.
''Muna da burin gyara yankunan da iftila'in ya rutsa da su zuwa ga yanayin da suka fi na baya, ta hanyar inganta ababen more rayuwa da gine-gine da kuma yanayin kayayyakin tarihinsu,'' a cewar Erdogan, yana mai jadadda kudurin gwamnatin na farfado da yankunan.
Ya kuma yi nuni kan muhimmacin daukar matakan kariya daga girgizar ƙasa, inda ya kara da cewa, '' Ba mu da wani zabi illa mu gaggauta mayar da biranenmu wurare da za su iya jure girgizar ƙasa musamman Istanbul.''
A tsokacin da ya yi kan girgizar ƙasa na baya-bayan nan a ƙasar Girka, Shugaban ya jaddada muhimmancin yin shiri, inda ya ce, “Girgizar ƙasar Girka tana tunatar da mu girmar kokarin da muke yi da kuma shiri kan girgizar kasa don ceton kasarmu."
Turkiyya dai na ci gaba da gudanar da ayyukanta na sauya fasalin birane, kana hukumomi na ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa garuruwan da ke fuskantar barazanar girgizar ƙasa a nan gaba, in ji shi.