‘Dole ne’ sahihin hadin kai da Swidin don yaki da ta’addanci'

‘Dole ne’ sahihin hadin kai da Swidin don yaki da ta’addanci'

Babu wata kasa da za ta zama mamban NATO ba tare da samun amincewar dukkan kasashen kawancen ba...
Cavusoglu / Photo: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewa ya zama wajibi a samu hadin kai ingantacce da Swidin don yaki da ta’addanci.

Cavusoglu ya bayyana hakan ga takwaransa na Swidin Billstrom a Brussels babban birnin Beljiyom yayin da ake gudanar da taron ministocin Harkokin Wajen Kasashe Mambobin NATO.

Minista Cavusoglu ya bayyanawa Billstrom abubuwan da Turkiyya ke son gani daga Swidin da ke bukatar zama mamban NATO.

Cavusoglu ya yi wani Karin haske ta shafinsa na Twitter bayan taron da Ministocin suka yi inda y ace “Mun jaddadawa Tobias Billstrom halayyar da muke son gani daga Swidin da ke son zama mamban NATO”.

Ya kuma ce “Sahihin hadin kai don yaki da ta’addanci ya zama dole”.

AA