Turkiyya kasa ce da ke da muhimmin matsayi a duniya, don haka dole fannin diflomasiyyarta ya yi karfi, a cewar shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan.
"Turkiyya tana tsakiyar nahiyoyi uku, samun karfinta a fagen-daga da kuma kan teburin lamuran duniya ba zabi ne a gare mu ba; wajibi ne," in ji Erdogan a jawabinsa ga jakadun Turkiyya da ke aiki a cikin gida da kuma kasashen waje a ranar Talata.
Jami’an diflomasiyyar Turkiyya sun hallara a Ankara babban birnin kasar domin gudanar da taron jakadu karo na 14 don tattauna batutuwan da suka shafi yankunan da suke wakilta da ci gaban kasa-da-kasa da sauyin yanayi da kuma kalubale da damarmaki da aka samu.
Shugaba Erdogan ya ce Turkiyya kasa ce da "dole a dama da ita" sannan ta kafa tarihi a huldar diflomasiyya la’akari da yadda take taka muhimmiyar rawa a batutuwan da suka shafi duniya kana kasashe da dama na kokarin koyi da halayenta.
Da yake waiwaye kan yaki da ta'addanci, Erdogan ya ce Turkiyya ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan tunkarar kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada da ASALA da PKK.
"Ba za mu wulakanta 'yancinmu da makomarmu a yakin da ake yi da ta'addanci ba," in ji Erdogan.
Ayyukan da Turkiyya ke yi zai ci gaba da gudana har sai ta kawar tare da fatattakar ‘’annobar ta’addanci’’ da ke barazana ga yankin Turkiyya da kuma Iraki, a cewar Erdogan.