Dakarun Turkiyya sun kwace manyan makamai da alburusai mallakar ‘yan ta’adda na kungiyar PKK a maboyarsu da ke kan iyakar kasar da arewacin Iraki, in ji wata sanarwa da Ma’aikatar tsaron Kasa ta Turkiyya ta fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa a yayin bincike a arewacin Iraki ne aka samu nasarar kwace alburusan bindiga samfurin AK-47 guda 10,800, alburusan babbar bindiga samfurin 6.62mm PKMS guda 720, alburusan bindiga samfurin DShK guda 120 da ma’aji’yar alburusan DshK guda 11.
Dakarun na Turkiyya sun kuma kwace gurneti guda takwas, sandar babbar bindigar DShK guda daya, gangar jikin bindigar DShK da kuma bindigun AK-47 guda hudu.
‘Yan ta’adda na PKK na yawan buya a sansanoninsu na arewacin Iraki inda suke kai wa Turkiyya hare-hare daga wuraren.
A shekaru sama da 35 da ta dauka tana kai hare-hare a Turkiyya, kungiyar PKK - wadda Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci, ta kashe sama da mutane 40,000 da suka hada da mata da yara kanana.