Cote d'Ivoire da Turkiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar ayyukan soji

Cote d'Ivoire da Turkiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar ayyukan soji

Turkiyya da Côte d'Ivoire sun sanya hannu kan yarjejeniyar ayyukan soji don ƙara haɓaka alaƙarsu.
Ministan Tsaron Kasa na Turkyya Yasar Guler da Ministan Tsaro na Uvory Coast Tene Brahima Outtara sun sanya hannu kan yarjejeniyar bayar da horo ga sojoji da hadin kai.

An sanya hannu kan yarjejeniyar cude-ni-in-cude-ka a ranar Talata a wajen baje-kolin SAHA EXPO na kayayyakin tsaro ta 2024, a Istanbul wanda shi ne baje-kolin kayan tsaro mafi girma a Turkiyya da ma Turai baki daya.

Sama da kamfanoni 1,400 daga kasashen duniya sama da 120 da wakilan kamfanonin saye da yar da kayayyaki na kasa da kasa 178, da wakilan gwamnati 312 ciki har da manyan jami'an ma'aikatu ne ke halartar baje-kolin.

Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta fitar da wata sanarwa ta shafin X inda ta ce "Ministan Tsaron Kasa na Turkiyya Yasar Guler ya gana da Ministan Tsaro na Ivory Coast, Tene Brahima Ouattara, wanda ke halartar baje-kolin SAHAA EXPO.

Bayan ganawar tasu, ministocin biyu sun sanya hannu kan Yarjejeniyar Horon Soji da Hadin Kai."

Ana sa ran yarjejeniyar za ta fadada ayyukan tsaro tsakanin Turkiyya da Côte d'Ivoire, ciki har da bayar da horo. Baya sanya hannun, Ministoci Guler da Ouattara sun baiwa juna tambarin kasashensu.

Habaka karfin soji

Masana'antar kayan tsaro ta Turkiyya ta shaida habaka cikin hanzari a shekaru 20 da suka gabata, inda ta zama mai taka muhimmiyar rawa a duniya.

Alakar tattalin arziki, tsaro da diflomasiyya tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka ta kara karfi a 'yan shekarun nan.

Kasashen Afirka da dama na amfani da kayan tsaron da Turkiyya ta samar, da suka hada da jiragen yaki marasa matuka, don yaki da barazanar tsaro.

Rundunar Sojin Turkiyya ta horar da dakarun kasashen Afirka da dama don haɓaka ayyukansu.

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Côte d'Ivoire a 2016, inda aka sanya hannu kan yarjeniyoyi tara a bangarorin tsaro, tattalin arziki, fasahar ƙere-ƙere da kayan more rayuwa.

TRT Afrika