Shugaba Erdogan ya ce yana fata zuwa ƙarshen 2024 a rinƙa samun ganga 100,000 ta fetur a kullum daga yankin Gabar. / Hoto: AA

Babban burin Turkiyya shi ne samun “cikakken ƴanci a ɓangaren makamashi,” kamar yadda Shugaba Erdogan ya bayyana.

“Babban burinmu shi ne samun cikakken ƴanci a ɓangaren makamashi. Mun kuduri aniyar aiwatar da ayyukan da za su tabbatar da ɗorewar makamashin Turkiyya,” kamar yadda Erdogan ya bayyana a jawabinsa na ranar Asabar a yayin wani taro da da Turkiyya ta shirya a lardin Zonguldak na Turkiyya da ke gaɓar Tekun Bahar Rum.

Erdogan ya ƙara da cewa adadin da rijiyar mai ta Tsaunin Gabar ke samarwa a kullum wadda ke a lardin Sirnak ya haura sama da ganga 35,000 a duk rana.

“Muna son a duk rana abin da za a samu a Gabar ya kai ganga 100,000 a duk rana zuwa ƙarshen 2024,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Erdogan ya kuma bayyana fatan sanar da sabon labari mai dadi a cikin lokaci mai zuwa game da man fetur, hakar ma'adinai, da iskar gas, yana mai karawa da cewa: "Ba za mu sake ba da damar hana amfani da albarkatun Turkiyya waɗanda ke ƙarƙashin ƙasa da na doron ƙasa ba.”

Tun daga 2020, Turkiyya ta haɓaka aikin da take yi na haƙo mai da iskar gas, haka kuma waɗannan ayyukan sun jawo an sake gano wasu albarkatun ƙasa a yankin Gabar da ke lardin Sirnak.

Matsayin da aka samu na samar da man fetur da sabbin ma'adinan ya kawo kasar kusa da burinta na samun 'yancin kai na makamashi.

AA