'Yan ta'addar PKK da rassanta na waje da suka hada da YPG na ci gaba da daukar mayaƙa yara ƙanana ta hanyar garkuwa da su wanda hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Dibar yara ƙanana ana saka su yaƙi, ya saɓa wa dokokin kasa da kasa, musamman ma Dokokin Majalisar Dinkin Duniya kan Hakkin Yara Kanana, amma kungiyar ta'addancin na ci gaba da diban yaran tana raba su da hakkin rayuwa.
PKK/YPG na ci gaba da aikata muggan laifuka na sace yara daga wajen iyayensu, duk da yarjejeniyar watan Yunin 2019 da MDD da daya daga shugabannin YPG, Ferhat Abdi Sahin (Mai lakabin Mazlum Abdi), suka sanya hannu a kai a Geneva don a saki yara kanana da ke tare da kungiyar.
A yayin da ake yaudarar matasan cikinsu, amfani da karfi da garkuwa ne hanyoyin da ake tafiya da kananan yara, sannan kungiyar na yi wa yaran da iyayensu alkawarin kudade, saboda suna cikin matsin tattalin arziki a Siriya da Iraki.
Wata majiya ta bayyana cewa PKK na daukar yara kanana da ƙarfin tuwo da sunan "wajabcin haraji" inda suke kokarin tabbatar da an ƙwaci yaro daya daga kowanne gida don yin aikin soji na wajibi.
Rashen "Matasan Juyin Juya Hali" na kungiyar ne ke da alhakin tabbatar da amfani da yara kanana a Siriya inda ake kama su ko garkuwa da su.
Daukar yara ta ƙarfi da yaji
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa a 'yan shekarun nan, shekaru 15 ne matsakaici na yaran da ke yaki tare da kungiyar, wadda ke ta kokarin cike giɓi da yara kanana.
Bayanan da wasu na cikin gida suka bayar sun bayyana cewa kungiyar ta'addancin na bayar da horo na akalla wata tara ga yara kanana, kuma don guje wa tantancewar kasa da kasa, ana yi wa yaran rajista da sunaye da sauran bayanan bogi.
'Yan ta'addar na kuma cin zarafin yara mata ƙanana, wadanda da yawansu suke mutuwa yayin kokarin guduwa daga sansanonin 'yan ta'addar, ko daga ƙunar baƙin wake da cututtuka, in ji majiyoyin.
Daukar yara kanana ta karfi da yaji a kwanakin nan ya janyo martani kakkausa a tsakanin Siriyawa, inda jama'a suke gudanar da zanga-zanga. Kungiyoyin 'yan ta'addar kuma na kokarin hana zanga-zangar ta hanyar amfani da karfi.
Wasu daga cikin iyalan da yaransu suke hannun 'yan ta'addar sun roki kasashen duniya da su dawo musu da yaransu gida.
Wasu lokutan kungiyoyin kasa da kasa na isa ga PKK/YPG, wadanda suke da sunan SDF a Siriya, su bukaci da su mayar da yara kanan da ke hannunsu ga iyalansu.
Rahotannin kasa da kasa
Rahotannin kasa da kasa da dama sun ambaci irin yadda kungiyar ta'addar ke ɗiban yara kanana.
A rahoton da Amurka ta fitar a 2016 kan fataucin mutane, an bayyana cewa "Reshen PKK a Siriya na PYD/YPG, na ci gaba da daukar yara maza da mata 'yan kasa da shekaru 15 a matsayin mayaka inda suke kai su sansanonin bayar da horo."
A wani rahoto da kan hakkokin dan adam na kasashe da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar mai taken 'Yara Sojoji', an bayyana cewa PKK na yawan daukar yara kanana, amma ba a bayyana adadin yaran ba.
A rahoton Yara da Yaki da Sakatare Janar na MDD ya gabatar ga Kwamitin Tsaro na Majalisar a watan Yunin 2015, an bayyana cewa "an dauki yara maza da mata 'yan kasa da shekaru 15 a kungiyar YPG/YPJ kuma an kai su fagen daga."
MDD a rahoton ta na shekara-shekara kan Yara da Rikici na tsakanin Janairu da Disamban 2022, ta bayyana sama da yara ƙanana 1,200 ne kungiyar ta yi amfani da su a matsayin sojoji.
Bayanan da aka buga sun bayyana cewa reshen PKK na Siriya SDF ya dauki yara kanana 637, inda SDF din da ke da alaka da PKK/YPG suka shigar da yara kanana 633 cikin mayaƙansu.
Asusun Kula da Yara na MDD ko UNICEF, watan Yunin 2014 ya fadi cewa "Abun damuwa ne matuka game da labaran da ake samu na cewa yara kanana na sahun mayakan PKK, wadda kasashen duniya suka amince da cewa kugiya ce ta ta'adda.
Amfani da yara kanana da kungiyoyin ta'adda ke yi ya saba wa dokokin kasa da kasa."
Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto a watan Yuni da ke bayyana YPG ta dibi yara kanana suna shiga yaki.