| Hausa
TURKIYYA
2 MINTI KARATU
Ƙarfin tsaron Turkiyya na iya dakatar da ta'addancin Isra'ila kan Falasɗinawa — Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ci gaban da Ankara ke da shi a ɓangaren tsaro zai iya ba ta ikon ƙalubalantar ta'addancin Isra'ila kan Falasɗinawa, inda ya bayar da misalin rawar da Turkiyya ta taka a yaƙe-yaƙen Karabakh da Libya.
Ƙarfin tsaron Turkiyya na iya dakatar da ta'addancin Isra'ila kan Falasɗinawa — Erdogan
Shugaba Erdogan ya bayyana cewa masana'antar tsaron Turkiyya riga-kafi ce. / Hoto: AA / Others
29 Yuli 2024

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ƙasarsa na iya kawar da ta'addancin da Isra'ila ke yi a kan Falasɗinawa, duba da yadda Ankara ke da masana'antar tsaro "mai ƙarfin gaske."

Da yake bayani a garinsu na Rize da ke arewa maso-gabashin Turkiyya a ranar Lahadi, Shugaba Erdogan ya jaddada cigaban da ƙasar ta samu a fannin masana'antun tsaro, ya kuma bayyana imanin da yake da shiga samun ƙarin ci gaba.

"Kamar yadda muka shiga Karabakh, kamar yadda muka shiga Libya, za mu iya yin irin wannan abu gare su. Babu dalilin ƙin yin hakan. Kawai muna son mu ƙara samun ƙarfi don yin hakan," in ji Erdogan.

Erdogan ya kuma ce Turkiyya ta tsayar da duk wata alaƙa ta kasuwanci da diflomasiyya da Tel Aviv don mayar da martani ga ta'addancin Isra'ila a Gaza.

Game da batun ziyarar Shugaban Gwamnatin Falasɗinawa Mahmoud Abba zuwa Turkiyya, Erdogan ya ce Ankara ce ta gayyace shi, amma Abbas bai amsa gayyatar ba.

Ya ƙara da cewa "Za mu ɗauki mataki na gaba yadda ya kamata."

MAJIYA:TRT World