"Mun tsaya tsayin daka wajen bin gaskiya, ba wai kasarmu kadai ba har ma ga walwalar bil'adama gaba daya," in ji Daraktan Sadarwa na gwamnatin Turkiyya, Fahrettin Altun.
Yayin da take magana kan kokarin Turkiyya wajen maganin labaran da ake shiryawa domin yin zagon kasa ga yunkurin sasantawa tsakanin Turkiyya da makwabciyarta Girka, “Cibiyar yaki da labaran karya ta Turkiyya ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen fitar da sakamakon bincikenta cikin harsunan Turkanci da Ingilishi da Girka inda ya ayyana labarin a matsayin na karya.”
Da yake gidan talabijin din Girka ANT1 ya watsa labarin ne a cikin shirin labaransa da aka fi kallo, inda ya yi ikirarin cewa "Turkiyya ta ci zarafin masuntan Girka a Kardak," tare da wasu bidiyoyi, cibiyar yaki da labaran karya ta Turkiyya ta gudanar da cikakken bincike, a cewarsa.
A sakamakon binciken, an bayyana cewa bidiyon da aka yi amfani da shi ya kai shekara uku da suka wuce.
“Masananmu, tare da jami'an tsaron bakin tekun Turkiyya, sun tabbatar da cewa ba a samu wata rashin jituwa ba kwanan nan kamar yadda rahoton mai yaudara ya nuna,” a cewar darakan watsa labaran.
“Labarin mai yaudara nan da nan ya ja hankalin mutane a shafukan sada zumunta, yana kokarin haddasa sabani tare da karkata ra'ayoyin jama'a a Girka,” in ji shi.
Bayan bayanin da cibiyar yaki da labaran karyar Turkiyya ta fitar, dole ya sa gidan talabijin din ANT1 ya gyara labarinsa.
“Lamarin ya nuna muhimmancin taka-tsan-tsan kan shirye-shiryen watsa labaran karya da ke kokarin katse kokarin diflomasiyya tare da zuzuta rashin jituwa tsakanin kasashe,” in ji Altun.