Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun buɗe wuta kan masu ibada a wata coci da ke gundumar Sariyer a birnin Santambul, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
A lokacin ibadu na ranar Lahadi a Cocin Santa Maria da ke unguwar Buyukdere, wasu mutum biyu ɗauke da makamai sun buɗe wuta kan waɗanda suka halarci cocin da misalin 11:40 agogon kasar, inda suka kashe mutum guda, kamar yadda Ministan Harkokin Cikin Gida Ali Yerlikaya ya bayyana a ranar Lahadi.
“Ana gudanar da babban bincike” domin kama waɗanda ake zargi, kamar yadda Yerlikaya ya bayyana a shafinsa na X inda ya kara da cewa: “Muna Allah wadai da wannan ɗanyen aikin.”
Bayan kai wannan harin, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi waya da gwamnan Gundumar Sariyer, Omer Kalayli da Faston Cocin Santa Maria Anton Bulai da Jakadan Poland a Istanbul Witold Lesniak.
Shugaban na Turkiyya ya kuma mika sakon ta'aziyyarsa da fatan alheri ga al'ummar cocin bayan afkuwar lamarin.
Ya tabbatar wa gwamnan Sarıyer, limamin coci, da karamin ofishin jakadancin Poland cewa ana daukar dukkan matakan da suka dace don kamo wadanda suka kai harin cikin gaggawa.