Dubban mutane ne suka yi gangamin goyon bayan Falasɗinu a Istanbul ranar farko ta shekarar 2025 yayin da yaƙin ƙare-dangin da Isra’ila ta ke yi a Gaza ke ci gaba:Hoto/ AA

Ɗaruruwan dubban mutane ne suka yi gangami a birnin Istanbul, inda suka halarci wani babban taron da gidauniyar matasan Turkiyya (TUGVA) ta shirya da maudu’in “Farkar da Duniya."

A cikin sa’o’in farko na sabuwar shekara ne dai, mutane da taken ‘Gadar Galata za mu je' suka fara taruwa bayan sun yi sallar Asuba a babban masallaci Aya Sofya domin nuna goyon bayansu ga Falasɗinawa.

Dubban mutane ne suka yi jerin gwano a Istanbul domin nuna goyon baya ga Falasɗinu ranar farko ta sabuwar shekara yayin da yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra’ila ke yi kan Gaza ke ci gaba.:Hoto/ AA

Da yawa daga cikin masu gangamin sun saka mayafin keffiyeh domin nuna goyon bayansu ga Gaza kuma sun riƙe kwalaye da rubuce-rubuce kamar "Birnin Ƙudus namu ne," da "Gaza: Inda Yara Ba Sa Girma," da kuma "Birnin Ƙudus na ƙarƙashin Mamaya."

Wasu kuma sun kunna fitilu yayin da suke gangamin, inda suke rera take kamar "Isra’ila mai kisan-kai za ta gurfana a gaban ƙuliya," da "Shahidai ba sa mutuwa," da kuma "Daga Istanbul zuwa Al-Aqsa, dubban gaisuwa ga ‘yan gwagwarmaya."

Bayan sun isa Gadar Galata, masu gangamin sun bi ta shingen ‘yan sanda kafin su shiga wurin taron.

Dubban mutane a Istanbul ne suka yi gangamin goyon bayan Falasɗinu a ranar farko ta sabuwar shekara yayin da yaƙin ƙare-dangin da Isra’ila take a Gaza ke ci gaba: Hoto/ AA

Ƙungiyoyi ba da agaji sun bai wa mahalarta taron shayi da gurasar simit da miya, yayin da hukumomi suka tabbatar da ingantaccen tsaro kusa da masallatan da gadar don tabbatar da da cewa koma ya tafi yadda ya kamata.

Wannan taron ya jaddada alaƙa ta tarihi da al’ada da ke tsakanin Turkiyya da Birnin Ƙudus da ma Masallacin Ƙudus inda mahalarta taron ke kira ga duniya ta ƙara sanin abin da ake ciki tare da ɗaukar mataki don agaza wa Falasɗinawa.

TRT World