Kamfanin kayan tsaro na Turkiyya mai suna Titra Technology ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin samar da jirage marasa matuka na Malaysia, Aeroyne Group don tallata Alpin, jirgin sama mai saukar ungulu mara matuki na farko kirar Turkiyya.
Titra na halartar kasuwar baje-kolin kayan tsaro ta ‘Langkawi International Maritime and Aviation Fair [or LIMA 2023]’ da ake ci gaba da gudanarwa.
Wanna baje-koli yana daya daga cikin na kayan tsaro mafi girma a yankin Asia-Pacific, kuma ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin Aerodyne Group, daya daga cikin kamfanoni da suka fi samar da jiragen yaki marasa matuka a duniya.
Za a samar da hadin kai da ya kunshi komai tsakanin Titra da Aerodyne, wanda kamfanoni ne da suka kware wajen samar da jiragen yaki marasa matuka.
Yarjejeniyar za ta fara mayar da hankali ga kasuwannin Malaysia, daga baya kuma za ta fada zuwa kasuwannin duniya.