Yerlikaya ya shaida wa manema labarai cewa ƴan sanda na iya ƙoƙarinsu domin magance lamuran. / Hoto: AA

Jami’an tsaron Turkiyya sun kama waɗanda ake zargi a wani hari da aka kai wata cocin Katolika a Santambul wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda, kamar yadda Ministan Harkokin Cikin Gida Ali Yerlikaya ya tabbatar.

“Mutum biyu waɗanda ake zargi da kisan wani ɗan ƙasarmu Tuncer Cihan a lokacin addu’o’i na ranar Lahadi a Cocin Sariyer Santa Maria, an kama su,” kamar yadda Yerlikaya ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi.

“Ina taya ƴan sandanmu na Santambul da kuma jaruman ƴan sandan da suka gano su tare da kama waɗanda ake zargin. Ina ƙara mika ta’aziyyata ga iyalai da ƴan uwan ɗan ƙasarmu wanda ya rasa ransa.

“Duka mutum biyun ƴan ƙasashen waje ne. Mun gano cewa waɗanda ake zargin -- ɗaya ɗan Tajikistan ne sai ɗaya kuma Rasha – kuma suna da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh,” in ji shi.

A ranar Lahadi ne wasu ƴan bindiga biyu suka buɗe wuta kan masu ibada a wata coci da ke Gundumar Sariyer inda mutum guda ya mutu, kamar yadda hukumomi suka tabbatar tun da farko.

A lokacin da yake Allah wadai da wannan “mummunan harin,” Gwamnan Santambul Davut Gul ya shaida wa manema labarai cewa wanda harin ya rutsa da shi shekararsa 52, bayan shi kuma babu wanda ya samu rauni.

Yerlikaya tun da farko ya tabbatar da cewa lamarin ya faru da misalin 11:40 na safe, agogon ƙasar.

Bayan kai harin, nan take ministan cikin gida na kasar ya tabbatar da cewa ana gudanar da bincike kan lamarin.

Zuwa yanzu dai babu tabbaci kan dalilin kai wannan harin. Ministan ya bayyana cewa akwai wuraren ibada da dama a Istanbul kuma ana gudanar da ibada a kowanen su cikin kwanciyar hankali.

Ya kara da cewa dukkanin al'ummar Turkawa sun yaba da wannan yanayi na tsaro.

“Masu kokarin kawo cikas ga hadin kai da hadin kan al’ummarmu ba za su taba yin nasara ba. Ina so na jaddada wannan,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

AA