An kashe ƴan ta'adda biyu a lokacin kai harin a ranar 6 ga watan Fabrairu. / Hoto: AA

Ministan Shari’a na Turkiyya Yilmaz Tunc ya ce an kama mutum 54 bayan an gudanar da bincike dangane da wani hari da ƴan ta’addan DHKP suka kai a farkon makon nan a Babbar Kotun Santambul da ke Caglayan.

Mutum 14 ake tuhuma da zargin “yunkurin kawo rashin zaman lafiya” da kuma “kisan kai,” sannan aka kama mutum 33 da hannu “a ƙungiyar ta’addanci” inda aka kama wani mutum ɗaya kuma kan zarginsa da taimaka wa “kungiyar ta’addanci,” kamar yadda ya rubuta a shafinsa na X a ranar Juma’a.

Tunc ya bayyana cewa an gano mutum biyar cikin shida waɗanda suka yi rubutu mai tayar da hankali a shafin sada zumunta inda aka kama su.

Haka kuma sanarwar ta ce akwai ɗan uwan ɗaya daga cikin maharan wanda ake yi wa shari’a a kotun a lokacin harin, wanda shi ma yana cikin maharan inda aka kama shi.

“Za mu ci gaba da yaki cikin azama kan dukkan kungiyoyin ta’addanci da ke son kawo cikas ga zaman lafiyar kasarmu da al’ummarmu,” kamar yadda Tunc ya bayyana.

An kashe wasu ‘yan ta’adda biyu da suka bude wuta a shingen binciken ‘yan sanda a ranar 6 ga Fabrairu a gaban Kotun Santambul.

An kashe mace ɗaya sannan kuma mutum shida daga sun samu rauni ciki har da ƴan sanda uku.

AA