An kai harin ta'addanci hedkwatar Masana'antar Kayayyakin Jiragen Sama ta Turkiyya TAI

An kai harin ta'addanci hedkwatar Masana'antar Kayayyakin Jiragen Sama ta Turkiyya TAI

Ofishin Babban Mai Shigar da Ƙara na Ankara ya ƙaddamar da bincike kan harin ta'addancin da aka kai wajen.
Hotunan talabijin sun nuna wata ƙofa da aka lalata da kuma arangama a wani wajen ajiye motoci da ke kusa.  / Hoto:  Ihlas Haber Ajansi 

An kai wani harin ta’addanci hedkwatar Masana’antar Kayayyakin Jiragen Sama ta Turkiyya (TAI) a birnin Ankara. Rahotanni sun ce an ji karar fashewar wani abu, sannan hotunan talabijin sun nuna yadda aka yi musayar wuta.

“Abin takaici, adadin wadanda suka yi shahada ya kai biyar, inda jumullar mutanen da suka ji rauni ya kai 22,” kamar yadda Ministan Cikin Gida Ali Yerlikaya ya shaida wa manema labarai

An tura jami’an ba da agajin gaggawa zuwa wajen. Hotunan talabijin sun nuna wata ƙofa da aka lalata da kuma arangama da ake yi a wani wajen ajiye motoci a kusa da wajen.

Yerlikaya bai bayyana cewa ga ƙungiyar da ta kai harin ba, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano ainihin wanda ya kai shi. Sai dai Ministan Tsaro Yasar Guler na nuna yatsa ga ƙungiyar ta’addanci ta PKK.

“Muna yi wa waɗannan lalatattun PKK ɗin hukuncin da ya cancance su a kowane lokaci. Amma ba sa shiga taiayinsu,” a cewar Guler.

“Za mu ci gaba da bin su har sai an kawar da ɗan ta’adda na ƙarshe.”

Ofishin Babban Mai Shigar da Ƙara na Ankara ya ƙaddamar da bincike kan harin na ta’addanci da aka kai wajen.

TAI na ɗaya daga kamfanonin tsaro mafiya muhmmanci na Ankara. Shi ne ya ƙera KAAN, jirgin yaƙin ƙasar na farko tare da sauran muhimman kayayyaki.

Allah-wadai daga ƙasashen duniya

Allah-wadai daga ƙasashen duniya sun biyo bayan harin a Ankara.

Shugaban Rasha shi ne jagora na farko da ya yi Allah-adai da harin sannan ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaban Turkiyya Recep tayyip Erdogan wanda yake a Kazan yana halartar taron BRICS.

Sakatar Janar na kungiyar NATO Mark Rutt da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres suma sun yi Allah-wadai da harin.

“Muna Allah-wadai da ta’addanci ta kowace fuskarsa da babbar murya, sannan muna sa ido sosai kan abubuwan da suke faruwa,” kamar yadda Rutte ta bayyana a shafin X.

Guterres ma ya miƙa ta’aziyya ga Turkiyya.

“Muna jiran bayanai amma mun yi Allah-wadai da hari kan fararen hula. Mun aike da ta’aziyyarmu ga iyalan waɗanda abin ya shafa, kuma muna fatan wadanda suka ji rauni za su samu sauki nan kusa,” a cewar Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq a madadin Guterres.

Pakistan ta yi Allah-wadai da harin na ta’addanci da “babbar murya”.

Da yake aike wa da “muhimmiyar” gaisuwarsa kan asarar rayuka, Shugaba Asif Zardari ya bayyana goyon baya ga gwamnati da al’ummar Tukriyya.

“Pakistan tana tare da cikakken goyon baya ga ‘yan’uwanta ‘yan Turkiyya maza da mata a wannan lokaci mai wahala. Muna miƙa ta’azaiyyarmu ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan hari na matsorata, kuma muna addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata,” a cewar Zardari.

Su ma Aljeriya da Jordan na daga ƙasashen da suka yi Allah-wadai da harin.

‘Amurka ta yi Allah-wadai da harin da babbar murya”

Gwamnatin Joe Biden ta yi Allah-wadai da babbar murya kan mummunan harin na ta’addanci da aka kai hedkwatar Masana’antar Kayayyakin Jiragen Sama ta Turkiyya (TAI)

Mai Magana da Yawun Majalisar Tsaron Fadar White House John Kirby ya miƙa jimamin Washington ga “mutanen da mummunan harin ya shafa a Ankara, ta Turkiyya.”

“A safiyar nan, muna miƙa addu’o’inmu ga duka waɗanda abin ya shafa da iyalensu da kuma jama’ar Turkiyya a wannan lokaci mai wahala,” kamar yadda ya shida wa manema labarai a wajen wani taro.

“Hukumomin Turkiyya kamar yadda suka faɗa suna binciken wannan a matsayin yiwuwar harin ta’addanci , amma yayin da ba mu san manufar kai harin ba ko ainihin wanda ya kai shi, muna Allah-wadai da babbar murya kan wannan mummunan aiki,” kamar yadda ya bayyana.

TRT World