Türkiye is “determined to continue all possible mediation efforts” on Ukraine, said Fidan. / Photo: AA

Dandangatakar Moscow da Ankara na tafiya daidai yadda ake so, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan a yayin ganawa da Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin a Moscow.

"Akwai matakan da za a dauka na kasuwanci," in ji Fidan a ranar Talata, kamar yadda majiyoyin diflomasiyya suka bayyana.

Fidan ya samu tarba daga Putin a Fadar Cremlin da ke Rasha, inda ya halarci taron BRICS, kuma ya yi tattaunawar diflomasiyya.

Turkiyya "na ci gaba da shiga tsakani" game da Ukraine, in ji Fidan.

Ya kara da cewa "Game da Siriya, muna yin iya kokarinmu don ci gaba da dabbaka manufofin zaman lafiya, wadanda ku shugabannin (Putin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan) kuke dabbakawa.

Ya kuma ce ya samu damar tattaunawa kan wadanan batutuwa a wajen taron na Moscow.

Gudunmawar Turkiyya wajen warware rikice-rikice

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi maraba da sha'awar da Turkiyya ta nuna na ayyukan BRICS da suka shafi kasashe masu tasowa.

Tabbas za mu goyi bayan wannan bukata tata don ta kasance tare da mu, mu kusanci juna, mu warware matsalolin da ke damun mu baki daya," in ji Putin a yayin ganawa da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan a Moscow.

Da yake zaburar da bangarorin biyu kan "kara zurfafa alakar" kasashen BRICS, musamman tare da yankunansu daban-daban, Putin ya kuma ce suna bukatar gyara ayyukansu a fagen kasa da kasa, wajen tabbatar da tsaro da ta'ammuli na tattalin arziki.

Da fari kasashen Barazil da Rasha da India da China da Afirka ta Kudu ne suka fara kafa BRICS, amma a yanzu kasashen Masar da Ethiopia da da Hadaddiyar Daular Larabawa sun shiga ƙawancen.

Yarjejeniyar jigilar hatsi ta Tekun Maliya

Putin ya kuma yaba wa Ankara bisa nuna sha'awar warware rikicin Rasha da Ukraine, wanda aka fara a watan Fabrairu 2022.

Putin ya ci gaba da cewa a dukkan duniya an yaba wa shugaban kasar Turkiyya Recep tayyip Erdogan bisa dawo da yarjejeniyar jigilar hatsi a Tekun Maliya a tsakanin 2022-2023 lokacin da duniya ke fama da matsalar abinci, ya kuma gode wa Fidan saboda goyon bayan tattaunawa tsakanin Moscow da Kiev.

Turkiyya ta samu yabo saboda rawar da ta taka ta musamman don ganawa da dukkan bangarorin biyu, tare da kokarinta na dawo da jigilar hatsi ta Tekun Maliya.

"Tare muka taka rawa mai mhimmanci wajen kawo karshen rikicin Siriya," in ji Putin, game da kokarin da aka yi karkashin shirin Astana don karfafa zaman lafiya mai dorewa da zai kawo karshen rikicin Siriya.

Ya kara da cewa "Ina tunanin zai zama abu mai kyau a ci gaba da aiki da tsarin Astana da yaki da ta'addanci da yin duk wani abu da ya ta'allaka da mu ta yadda yanayin zai koma yadda ya kamata, wannan shi ne mafi muhimmanci gare mu."

Putin ya ci gaba da cewa "Mun lura da karsashi da aniyar abokanmu na Turkiyya wajen ganin sun bayar da gudunmawar warware rikice-rikice, ciki har da rikicin Ukraine."

Alaƙa da juna

Game da Alakar Rsha da Turkiyya, Putin ya ce Moscow ta gamsu sosai da alakarta da Ankara.

"Duk wannan na faruwa ne karkashin shugabanci da goyon bayan abokinmu, shugaban Jumhuriyar Turkiyya.

Da yake bayyana samun raguwa a bangaren alakar kasuwanci a wannan shekarar, Putin ya ce wannan na da alaka da yadda Rasha ta yi gyara kan farashin kayan da take saya daga kasashen waje da wadanda take fitarwa.

Ya kuma ce "Ina fata cewa za mu samu damar gyara wannan yanayi a nan kusa kuma komai zai bunkasa ta wannan hanya kamar dai yadda yake a shekarar da ta gabata," in ji Putin.

TRT World