Kafofin watsa labarai da ke ƙarƙashin ƙungiyar na da mabiya aƙalla mutum biliyan 3.5 ./ Hoto: AA

Mambobin ƙungiyar kafofin watsa labarai da ke yankin Asia da Pacific wato ABU, sun taru a birnin Istanbul na Turkiyya domin nazari dangane da yadda ƙirƙirarriyar basira ke kawo sauyi ga kafafen watsa labarai.

Ƙungiyar ta ABU ita ce ƙungiyar kafafen watsa labarai mafi girma a duniya mai mambobi 230 daga ƙasashe 65. Taron wanda kafar watsa labarai ta TRT ta shirya, shi ne babban taron ƙungiyar karo na 61 wanda ke da laƙabin “The Nexus of AI, Broadcasting and Society”.

An gudanar da jerin tattaunawa masu muhimmanci a ranar Lahadi a ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na TRT Mehmet Zahid Sobaci, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ta ABU tun daga shekarar 2023.

“Mun zo nan ne domin tattaunawa kan matsalolin da ake fuskanta a kafafen watsa labarai, mu yi musayar ra’ayoyi da kuma ɗaukar matakai waɗanda za su ƙara gyara makomar ABU,” kamar yadda ya bayyana a wani jawabi da ya yi a rana ta uku ta taron.

Taron shugaban ƙungiyar ta ABU da tattaunawar da mambobin gudanarwa na ƙungiyar suka gudanar da kuma tattaunawa tsakanin mambobin ƙungiyar, sun ƙara bitar tsare-tsare da matakai na shekara uku na ƙungiyar.

Haka kuma jami’an Turkiyya sun gudanar da tattaunawa tsakanisu da wakilai daga ƙasashen Indonesia da Mongolia domin lalubo hanyar da za a ƙara yauƙaƙa dangantaka ta ɓangaren kafafen watsa labarai.

An gudanar da taron waƙe-waƙe na ABU a ɗakin taro na Lutfi Kirdar da ke birnin Istanbul na Turkiyya a ranar Talata, inda a wurin taron, an samu mawaƙa daga ƙasashe 11 da ke yankin na Asia da Pacific.

A wurin taron, daraktan watsa labarai na Turkiyya Fahrettin Altun da Shugaban TRT wanda kuma shi ne Shugaban ABU Mehmet Zahid Sobaci da kuma Sakatare Janar na ABU Ahmed Nadeem duk sun yi jawabi.

Dukansu sun yi jawabi kan tasirin ƙirƙirarriyar basira da kuma kayayyakin watsa labarai na zamani da kuma irin ƙalubalen da ɓangaren watsa labarai ke fuskanta a yau.

TRT World