A shirye Turkiyya take ta taimaka wurin sasanta rashin jituwar da ke tsakanin Rwanda da DRC: Erdogan

A shirye Turkiyya take ta taimaka wurin sasanta rashin jituwar da ke tsakanin Rwanda da DRC: Erdogan

Erdogan ya kuma jinjina wa yunƙurin Rwanda na yaƙar 'yan ta'addan ƙungiyar FETO.
Tun daga shekarar 2022 'yan tawayen M23 ke tayar da ƙayar baya a gabashin Kongo. / Hoto: AA

Turkiyya ta ce a shirye take ta ba da duk wani tallafi da ake bukata domin warware takaddamar da ke tsakanin Rwanda da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, idan bangarorin biyu suna so, in ji Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

"Mu a matsayinmu na Turkiyya, a shirye muke mu ba da duk wani goyon bayan da ya dace don warware wannan batu (rikicin da ke tsakanin Rwanda da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo) wanda zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da zaman lafiya a tsakaninsu, idan bangarorin biyu sun yi fatan hakan,” kamar yadda Erdogan ya shaida wa taron manema labarai na hadin gwiwa a ranar Alhamis da takwaransa na Rwanda Paul Kagame da ke ziyara a Ankara babban birnin kasar.

Tun a shekara ta 2022 ne 'yan tawayen M23 suka kaddamar da hare-hare a gabashin Kongo. Kinshasa da wasu ƙasashen na zargin makwabciyarta Rwanda da mara wa ƙungiyar baya, zargin da Kigali ta musanta.

Erdogan ya kuma jinjina wa yunƙurin Rwanda na yaƙar 'yan ta'addan ƙungiyar FETO.

FETO ce ummul'aba'isin yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Turkiyya na 15 ga Yulin 2016, inda mutnae 252 suka halaka sannan 2,734 suka jikkata.

Turkiyya ta zargi FETO da kitsa wani kamfe na yi wa ƙasar zagon-ƙasa, ta hanyar shigar da mambobinta cikin hukumomin Turkiyya, musamma na soji, 'yan sanda da na shari'a.