A yayin da Isra'ila ke ci gaba da mummunan yaki a Gaza ba tare da nuna alamun dakatawa ba, TRT World ta shirya sakin wani shirin fim na bincike mai taken Holy Redemption, a ranar 24 ga watan Agusta a Atlas Cinema da ke gundumar Beyoglu ta Istanbul.
Fim din, yana karin haske ne kan mummunan bangare na yakin da ba a magana a kai - yadda Yahudawa 'yan kama guri zauna ke ƙwace filaye da gonakin Falasdina a karkashin inuwar yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda tun 7 ga Oktoba ya kashe Falasdinawa 40,000 mafi yawan su mata da yara ƙanana.
A watan Disamban shekarar da ta gabata, watanni bayan fara zubar da jini a Gaza, Sashen Binciken Kwakwaf na TRT World ya samu damar shiga wani waje mai muhimmanci amma wanda aka manta da shi: Yammacin Gabar Kogin Jordan.
Wadanda suka shirya fim din Holy Redemption sun gana da masu fafutuka 'yan Isra'ila, mambobin majalisar dokoki ta Knesset tare da shiga cikin kungiyoyin Yahudawa 'yan kama guri zauna, ciki har da kungiyar 'yan daba ta Masasan Hiltop, wadanda aka jibge su a kowanne bangare suna dauke da makamai tare da azamar sai sun kafa babbar kasar Isra'ila.
Ta hanyar tattaunawa da zuzzurfan bincike, fim din ya gano aniyar Isra'ila ta yin mulkin mallaka da wani ƙullallen shiri tsakanin shugabannin kasar da gungun Yahudawa 'yan daba.
Wadannan kungiyoyi na aiki tare - kowanne na aikata ta'asa karkashin baki kuma mummunan shirin ƙwace filaye da gonakin Falasdinawa suna tsugunar da su.
Mai fafutukar zaman lafiya na Amurka Medea Benjamin ya bayyana shirin fim din a matsayin "mummunan mari a kumatu" ga mamayar Isra'ila ke yi ga Falasdin.
"Fim din na bayyana gaskiyar lamari game da matasan Isra'ila 'yan daba da ɓarayi masu nuna wariya da ke kutsa kai ƙauyuka, suna ƙona gidaje, suna dukan manoma, suna lalata rayuwarsu ta yau da kullum, da ƙirƙirar rikici don korar Falasdinawa daga kasarsu. Kuma wannan na faruwa ne yau ba wai a 1948 ba," in ji Benjamin.
A ƙwacen filaye da gonakin da ake yi ta ci barkatai, fim din ya gano wasu salo masu bakanta zuciya - yadda jami'an tsaro da ke zama a shingayen binciken ababen hawa suke taimaka wa 'yan kama guri zauna wajen ƙwace yankunan Falasdinawa.
A wajen nuna shirin fim din, TRT World za ta karbi bakuncin tattaunawa bayan an nuna fim din.
A tattaunawar, sanannun 'yan jarida, masu fafutuka da malaman jami'a daga kasashen duniya daban-daban ne za su halarta, sannan akwai manyan mutane irin su Farfesa Bayahude-Dan Ingila Ilan Pappe, dan gidan likitan Canada da ya kubuta daga yakin Holocaust, Gabor Mate, marubuci kuma mai fafutuka Aaron Mate.
Akwai kuma Mai fafutuka dan kasar Australia kuma masanin tarihi Robert Marti da ɗan jaridar Isra'ila Gideon Levy da Malamin Jami'a Bafalasdine Farfesa Sami Al-Arian.
Sai mai fafutuka ɗan Amurka Medea Benjamin da ma'aikacin jiyya dan Falasdinu da Amurka, Ahmed Kouta wanda ya je Gaza a lokacin yakin da ake yi da mai fafutuka dan kasar Falasdinu Issa Amro.
Wadannan mutane za su tattauna tare da bayyana zuzzurfan tunani kan yadda Isra'ila ke mamaye yankunan Falasdinawa da yi musu kisan kiyashi.
'Yan jaridar TRT World sun ji ta bakin mutane ta hanyar shiga hatsari babba, saboda mummunar halayyar 'yan kama guri zauna da za su iya yi musu hauka.
Fim din ya kuma tabo hare-haren ta'addanci da kokarin cinna wa kauyuka wuta da cin zarafi kan mai uwa da wabi da kuma yanayi mummuna da Isra'ila ta jefa Yammacin Gabar Kogin Jordan da kauyuka a ciki.
Tattaunawar da kuma nuna shirin fim din za su gudana a mashahuriyar sinima ta 'Atlas Cinema' da ke gundumar Beyoglu a Istanbul a ranar 24 ga Agusta da misalin karfe 3 na yamma, kuma dukkan 'yan jarida na iya halarta.