Mamban kwamitin gudanarwa na ƙungiyar AC Milan ta Italiya, Zlatan Ibrahimovic ya amince da ƙudurin ƙungiyar na ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United, Marcus Rashford a matsayin aro.
Milan wadda ke mataki na 8 a teburin Gasar Serie A, tana fafutukar neman haziƙin ɗan wasan gaba da za ta aro har zuwa ƙarshen kakar bana.
Rashford dai yana cikin wani yanayi na rashin tabbas a ƙungiyarsa da ke Ingila, tun bayan zuwan sabon Koci Ruben Amorim, wadda har ta kai ɗan wasan ya bayyana sha'awarsa ta barin United.
Ana sa ran Rashford zai bar Old Trafford a kasuwar cinikin 'yan wasan ta Janairu nan, bayan rasa buga wasa biyar a jere, bayan da kocin ya ƙi saka shi a wasan da suka yi kunnen doki da Liverpool a Lahadin nan.
An yi ta raɗe-raɗin Rashford zai koma ƙungiyoyi daban-daban, ciki har da AC Milan, waɗanda rahotanni ke cewa tuni suka tuntuɓi United kan yiwuwar aro ɗan wasan mai shekara 27.
Albashi mai tsoka
Shafin Goal ya ambato Jaridar Calciomercato na cewa Ibrahimovic wanda a yanzu jami'in gudanarwa ne na AC Milan, ya amice da yunƙurin kawo Rashford zuwa Italiya.
Ibrahimovic tsohon gwarzon AC Milan ne, wanda ya taka leda a manyan ƙungiyoyin Turai da Amurka, ciki har da United, inda ya yi wasa tare da Marcus Rashford.
Rashford zai iya barin United a matsayin aro, duk da akwai tsoron cinikinsa ya zama mai rikici saboda albashinsa na maƙudan kuɗi, wanda ya kai fam dubu dari uku da sha biyar (£315,000) duk mako.
Jaridar ta ruwaito cewa tuni Milan ta amince ta biya ɗaukacin albashin, kuma za su gabatar da tayi a hukumance na ɗauko Rashford cikin kwanaki masu zuwa.
Akwai rahotannin da ke cewa Rashford ya yi fatali da tayin da ƙungiyoyi a Saudiyya suka yi na ɗauko shi, saboda yana son ci gaba da wasa a Turai, da kuma ci gaba da zama a tawagar ƙasarsa ta Ingila.
A yanzu dai za a saurari wasan Manchester United na gaba, inda za ta kara da Arsenal a Gasar kofin FA ranar Lahadi, don ganin ko Koci Amorim zai dawo da Rashford cikin tawagarsa.