Za mu yi abin da ya kamata domin doke Man City — Kocin Man U

Za mu yi abin da ya kamata domin doke Man City — Kocin Man U

Ten Hag ya ce “dole mu yi wasan gwanaye idan muna son mu hana City cin Kofin.”
Kocin Manchester United ya ce kungiyarsa ba za ta bai wa Manchester City damar cin manyan kofuna a kaka daya ba/Hoto:Reuters

Kocin Manchester United, Erik Ten Hag, ya ce 'yan wasansa za su yi duk abin da za su domin doke Manchester City a wasan karshe na gasar FA.

Da yake magana bayan kungiyarsa ta samu gurbin zuwa wasan karshe na gasar Kofin Kalubale na Ingila, Ten Hag ya ce “dole mu yi wasan gwanaye idan muna son mu hana City cin Kofin.”

“Za mu iya yin hakan. Mun tabbatar da hakan. Amma ba abu ne mai sauki ba. Babbar kungiyar ‘yan wasa ce (Man City), amma mu ma muna da manyan ‘yan wasa. Kuma za mu iya doke su,” a cewarsa bayan kulob dinsa ya doke Brighton da 7-6 a bugun fenareti.

A wasan dab da na karshen da Machester United ta yi da Brighton sai da aka kammala wasan minti 90 aka kuma kara miniti 30, amma ba a samu wanda ya ci ko kwallo daya ba, sannan aka shiga bugun fenareti.

Yadda yaran Pep Guardiola a Manchester City ke murza leda a kakar bana ya sa ana ganin zai yi wuya Manchester United a karkashin Erik Ten Hag ta iya tare guguwar City/Hoto:Reuters

Ita kuwa Machester City da doke Sheffield United cikin minti 90 ne da ci uku da nema ne a wasan dab da na karshen da suka yi inda Riyad Mahrez ya zura kwallaye uku a ragar Sheffield.

“Magoya bayanmu su kwantar da hankalinsu. Za mu duk abin da za mu iya don yin nasara kan Man City.”.

Manchester City tana farautar manyan kofuna uku a wannan kakar: Kofin Zakarun Turai da Kofin Gasar Firimiya da kuma Kofin FA na Ingila.

A Kofin Zakarun Turai Manchester City ta kai wasan dab da na karshe inda za ta kara da Real Madrid ranar 9 da ranar 17 ga watan Mayu.

A gasar Firimiya kuma kungiyar tana mataki na biyu da maki 70 yayin da take da kwantan wasa biyu. Idan ta yi nasara a wasanni biyun da suka rage, za ta iya lashe kofin gasar Firimiyar.

Za a gama gasar Firimiya a karshen watan Mayu yayin da za a kammala gasar FA ta Ingila a watan Yuni.

TRT Afrika da abokan hulda