Mbappe ya bar PSG ne bayan ƙarewar kwantiraginsa, inda ya tafi Real Madrid. / Hoto: AP

Sashen shari'a na Hukumar Ƙwallon Ƙwararru ta Faransa, Professional Football League zai ƙaddamar da bincike kan batun zargin da Kylian Mbappe ya yi cewa yana bin tsohon kulob ɗinsa, Paris Saint-Germain bashi.

Shafin Goal.com ya ruwaito jaridar L'Equipe tane cewa hukumar ta LFP ta shirya gudanar da binciken zargin da Mbappe ya yi kan PSG, cewa yana bin su euro miliyan €55.

Rahotanni sun ce hukumar ta tattara takardu daban-daban da za ta yi bincike kansu, kuma za ta nemi bahasin kowane ɓangare don ya bayyana matsayinsa.

Masu wakiltar Mbappe sun ce tuni sun gargaɗi PSG cewa dole ta biya albashinsa zuwa 30 ga Yuni, amma sai hakan bai faru ba.

Wannan dalilin ne ya tilasta wa ɗan wasan da a yanzu yake buga wasa a Real Madrid bayan ƙarewar kwantiraginsa da PSG, ya umarci lauyoyinsa su shigar da ƙorafi gaban hukuma.

Zuwa yanzu Mbappe ya buga wasanni biyu a gasar La Liga ta Sifaniya, duk da bai samu cin ƙwallo ba. Amma dai ya ciyo wa Madrid ƙwallo a wasansa na farko a kofin UEFA Super Cup, wasan da suka doke Atalanta da ci 2-0.

TRT Afrika