Vitor Osimhen ya bayyan aniyarsa ta barin Napoli ta Italiya. / Hoto: AFP

Ƙungiyar Paris Saint-Germain ta Faransa tana farautar ɗan wasan da zai maye gurbin gwarzon ɗan wasanta Kylian Mbappe wanda ya koma Real Madrid ta Sifaniya.

PSG ta mayar da hankali kan gwarzon ɗan wasan Nijeriya da ke taka leda a Napoli ta Italiya, wato Victor Osimhen, da kuma Khvicha Kvaratskhelia ɗan ƙasar Georgia.

Yayin da yunƙurin ɗauko Kvaratskhelia ya ci tura, PSG ta mayar da hankali kan kawo Osimhen, amma shi ma tattaunawarsu ta samu tasgaro.

A yanzu rahotanni na cewa dole sai PSG ta sayar da ko dai Gancalo Ramos, ko Randal Kolo-Muani kafin ta iya sayo Osimhen. Sai dai babu ɗaya cikin 'yan wasan da yake da niyyar barin kulob ɗin, wanda ya janyo yunƙurin kawo Osimhen ya samu tsaiko.

Ana tababar ko Victor Osimhen zai ci gaba da buga wasa a Napoli, ganin cewa sabon kocinsu yana neman kawo Rumelu Lukaku.

Sai dai idan PSG ta gaza ɗauko shi, Osimhen zai ci gaba a Napoli duk da dai akwai raɗe-raɗin Chelsae da wasu kulob a Saudiyya na kwaɗayin samun sa.

A yanzu dai Osimhen bai bi sahun sauran 'yan wasan a wasannin share fagen kakar baɗi ba.

TRT Afrika