'Yan wasan Leicester City biyu 'yan asalin Ghana, Jordan Ayewa da Abdul Fatawu sun samu rauni a wasan da tawagar ƙasarsu Black Stars ta Ghana ta buga na neman cancantar shiga gasar ƙasashen Afirka ta AFCON 2025.
Sai dai shi Fatawu zai rasa damar buga wasa har zuwa ƙarshen kakar bana, sakamakon raunin da ya samu a tantanin gaɓarsa, yayin wasan da suka kara da Angola tun a ranar Juma'a 15 ga Nuwamba.
Manajan Leicester City ta Ingila, Steve Cooper ne ya sanar da labarin doguwar jinyar da Fatawu zai yi, a ranar Alhamis, inda ya ce, "Raunin babba ne. Ya samu raunin tantanin gaɓa wanda zai hana shi wasa a kakar bana."
Da yake magana gabanin wasansu da Chelsea na ranar Asabar, Cooper ya faɗa wa 'yan jarida cewa, "Wannan babbar matsala ce, mafi muhimmanci gare shi saboda shi matashin ɗan wasa ne, ga shi kuma babban rauni ne."
Ɗan wasan mai shekaru 20 ya bugawa Leicester a duka wasanni 11 da ta buga a kakar bana, bayan da a kakar bara aka ba shi kwantiragi a ƙungiyar, kasancewar a baya ya zo aro ne daga Sporting.
Fatawu ya ci ƙwallaye shida a wasanni 40, inda ya taimaka wa Leicester ta yi nasarar dawowa ajin Firimiya daga ajin Championship.
Ayew zai dawo da wuri
Shi ma Jordan Ayew ɗan wasan gaba na Leiscester, ya samu rauni a wasan da tawagar Ghana ta yi canjaras da Angola da ci 1-1, inda Ghana ta gaza samun cancantar buga AFCON ta baɗi.
Sai dai kocin Leicester ya nuna kyakkyawan fata kan warkewar Ayew, da dawowarsa filin wasa, ba kamar Fatawu ba.
Cooper ya ce, "[Raunin Ayew] Ba babban rauni ba ne. Fatan shi ne zai iya dawowa wasa a ƙarshen mako".
Leicester tana mataki na 15 a teburin Firimiya da maki 10 bayan wasanni 11. Wasanta na gaba za ta kara ne Chelsea a gida.