Gawurtattun ƙungiyoyi biyu mafi suna a Sifaniya, wato Real Madrid da Barcelona, za su yi karawarsu ta farko a gasar LaLiga ta 2024-25, wasan da aka saba kira da El Clasico.
Wasan da za a buga gobe Asabar a gidan Madrid, Santiago Bernabeu zai yi zafi sosai, musamman ganin tazarar maki uku ne ke tsakanin ƙungiyoyin.
Nasarar Madrid za ta iya kawar da tazarar, yayin da akasan haka zai bai wa Barca gagarumin fifiko na maki shida a teburin LaLiga. Idan kuma suka yi canjaras, bambancin nasu ba zai canza ba.
A ɓangaren Real Madrid, masoya ƙungiyar na alfahari da haziƙin ɗan wasa Vinicius Jr, wanda ke kan ganiyarsa, wanda kuma ake ganin shi zai lashe kyautar Ballon d'Or ta bana da za a bayar a makon gobe.
Baya ga Vini wanda ya zura ƙwallaye uku rigis a wasansu da Borussia Dortmund a gasar Zakarun Turai da aka yi makon nan, Madrid tana tunƙaho da zaƙaƙuran 'yan was irinsu Kylian Mbappe da Jude Bellingham, waɗanda ake ganin za su fid da su kunya.
Matasan Barca
Sai dai a nata ɓangare, Barcelona na taƙama da matashin ɗan wasan da ya fi kowanne tsada a Sifaniya a halin yanzu, wato Lamine Yamal ɗan shekara 17, wanda zuwa yanzu yake da ƙwallaye biyar da tallafin ƙwallo bakwai a wasanni 13.
Sai dai a tarihin wasanni uku da Barca ta bugu da Madrid tare da Yamal, Barca ta yi rashin nasara a duka wasannin. Wannan zai iya tunzura Yamal ya ga ya sauya wannan tarihi.
A wasan Barca na ƙarshe-ƙarshen nan, tare da Bayern Munich sun yi nasara da ci 4-1, Yamal ya ba da tallafin ƙwallo guda, kuma ya maimaita hakan a wasansu da Sevilla inda suka lashe da ci 5-1.
Yayin da Barca ke shirin dira a gidan Madrid, akwai ɗan wasanta da ke wuta a halin yanzu, Raphinha ɗan asalin Brazil, wanda ya shiga jerin 'yan wasa 105 da suka taɓa cin ƙwallo uku a wasa, wanda ya yi a wasan da suka doke Munich ranar Laraba.
Ƙarƙashin jagorancin sabon koci Hansi Flick, ɗan wasan mai shekaru 27 ya ci zunzurutun ƙwallaye 9 da tallafin ƙwallo shida a wasanni 13 a kakar bana.
A wasan kece rainin na El Clasio, Barca tana da dattijon gwanin zura ƙwallo, Robert Lewandowski, wanda ke jan ragama a yawan ƙwallaye a LaLiga da ƙwallo 12 bayan wasanni 10.
Kowanne cikin Real Madrid da Barcelona na burin riƙe jagorancin teburin LaLiga tun a yanzu. A bara Madrid ce ta ɗauki kofin da tazarar maki 10 daga Barca wadda ta take mata baya.