Williams ne ya zura kwallon farko a wasan a cikin mintuna 47 da fara wasa/Hoto: Reuters   

Matashin ɗan wasan ƙwallon kafa na kulob ɗin Atletico Billao na ƙasar Sifaniya, Nico Williams Jr., yana ci gaba da murnar lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasa a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka kammmala ta shekarar 2024 a birnin Berlin na ƙasar Jamus.

Williams Junior., wanda iyayensa ‘yan asalin ƙasar Ghana ne, ya fito a matsayin ɗan wasan tsakiya a tawagar Sifaniya da ta yi nasara a wasan da ta kara da Ingila a filin wasa na Olympics a Berlin.

"A halin yanzu, ba mu san gagarumin abin da muka yi ba, burin kowane ɗan wasan ƙwallon shi ne kafa tarihi irin wannan. Wannan ƙyautar na sadaukar da shi ga duk wanda ya yarda da ni tun daga farko. Na yi farin ciki sosai saboda mun kafa tarihi," in ji Williams jim kadan bayan karbar ƙyautar.

Williams ne ya zura kwallon farko a wasan cikin mintuna 47 da fara wasa, bayan da Yamal Lamine, ɗan asalin Equatoguine da Maroko ya taimaka.

Zazzafar fafatawar ƙarshe

Ingila ta yi canjaras ne bayan da Cole Palmer ya buga kwallon a wajen raga a mintuna 73 da wasan.

Daga karshe dai Mikel Oyarzabal ne ya ci wa Sifaniya wasan a minti na 86.

Da yake magana game da wasan, Kwamitin Kula da Fasaha na UEFA wanda ke da alhakin yanke hukunci kan wanda zai ƙarbi ƙyauta a wasan ya ce: ''Ya kasance ɗan wasa mai zazzafar fafatawa tare da kare gidansa, ya rufe Marc Cucurella kuma ya koma tsakiyar fili inda ya haɗu da Dani Olmo. Ya zura ƙwallon farko sannan ya kasance ɗaya daga cikin 'yan wasa mafi fafatawa a filin wasan.''

''A koyaushe ina iya ƙokari don taimaka wa ƙungiyar tawa. A zahiri sai yanzu mutane suka soma sani na kuma suke ƙara girmama ni; ina jin daɗin wannan girmamawa matuka. Ina aiki a kowace rana don zama ɗaya daga cikin jajirtattu,'' in ji Williams.

'Yan wasan Sifaniya, da masu gudanarwa, da kuma magoya bayanta za su yi murnar samun nasarar lashe kofin Turai karo na huɗu a tsawon yayin da har yanzu Ingila ke ci gaba da neman damar lashe kofin Turai na farko.

TRT Afrika da abokan hulda