Wasanmu da City ba zai tabbatar da wanda zai lashe Gasar Firimiya ba —Arteta

Wasanmu da City ba zai tabbatar da wanda zai lashe Gasar Firimiya ba —Arteta

Arteta ya ce ko Arsenal ta yi nasarar doke City, wasanni biyar da ke gaba na cike da rashi tabbas.
Arteta ya ce yaransa sun yarda da kansu /Hoto:Reuters

Karawa tsakanin Manchester City da Arsenal ba za ta tabbatar da wanda zai lashe gasar Firimiya ba, in ji kocin Arsenal, Mikel Arteta.

Arsenal ce a saman teburin gasar Firimiya da maki 75, yayin Manchester City ke biye da ita da maki 70.

Sai dai City tana da kwantan wasa biyu yayin da Arsenal ta tashi canjaras a wasannin uku a jere.

Kungiyoyin biyu za su kara a Etihad ranar Laraba.

Wasu na ganin karawar tasu ce za ta tabbatar da wanda zai lashe gasar Firimiya.

“Mun san dole za mu je Etihad, zai kasance wani abu mai wuya, shin karawar ce za ta tabbatar da wanda zai lashe gasar? A’a,” a cewar Arteta.

Ya ce ‘yan wasansa sun yarda da kansu ganin yadda suka farke kwallaye biyu cikin kankanin lokaci a wasansu da Southampton.

“Amma dole su murza leda kamar gwanaye, abin da nake bukata kenan a wannan lokacin cikin wannan kakar,” in ji Arteta.

Arsenal ta tashi 3-3 da Southampton wadda ke kasan teburin Firimiya bayan Liverpool da West Ham sun rike ta Canjaras a jere.

"Idan muka yi nasara gobe ba mu lashe gasar ba. Zai iya rage yawan aikin da ke gabanmu, amma wasanni biyar a wannan gasar abubuwa ne masu cike da rashin tabbas," a cewar Arteta .

"Mun sani tun daga farkon kakar nan cewar City da Liverpool kungiyoyi ne masu karfin gaske, abubuwan da suka yi cikin shekaru shida zuwa bakwai da suka wuce sun cancanci yabo a kansu. Mun so mu cike gibin da ke tsakaninmu."

TRT Afrika da abokan hulda