Kocin da Arsenal, Mikel Arteta, da kocin Southampton, Ruben Selles, sun ce suna da kwarin gwiwar nasara a karawar/Photo Reuters

Arsenal da Southampton za su kara a gasar Firimiya a yau inda ita Arsenal za ta nemi karfafa matsayinta a saman teburin gasar yayin da Southampton za ta nemi ficewa daga rukunin kungiyoyin da za su koma gasa ta kasa da Firimiya.

Arsenal, wacce za ta karbi bakuncin Southampton, tana saman teburin gasar Firimiya da maki 74 yayin da Manchester City da ke bin ta ke da maki 70 da dakon wasa daya.

Idan City ta yi nasara a wasa dayan ratar da ke tsakaninta da Arsenal za ta koma daya tilo.

Mancesher City na barazanar kwace saman teburin gasar Firimiya daga Arsenal/Photo:Reuters

Wannan na nufin Arsenal za ta iya rasa matsayinta na saman teburi a duk lokacin da ta kasa yin nasara a wasannin da suka rage mata a kakar bana ta gasar firimiya idan City ta yi nasara a wasannin da suka yi mata saura.

Shi ya sa wasan da za a yi da yammacin Juma’a ke da muhimmanci ga Arsenal wadda ta barar da maki hudu a karawa biyun da ta yi ta baya bayan nan a cikin gasar.

Yadda kungiyoyin suke

Sai dai kuma Arsenal tana da tarihi mai kyau wajen karbar bakuncin Southampton. Arsenal ba ta sha kaye ba a karawa 27 da ta yi da Southampton a gidanta.

Arsenal ta barar da maki hudu cikin karawa biyu da ta yi a baya bayan nan a cikin gasar Firimiya/Photo:Reuters

Kuma yaran Mikel Arteta ba su taba shan kaye a gida a wannan kakar ba sai lokacin da Man City ta doke su 3-1 a watan Fabrairu.

Ita kuwa Southampton tana kasan teburin gasar Firimiya da maki 23, kuma kungiyoyin Leicester City da Nottingham Forest da kuma Everton da ke samanta suna da maki 25 da maki ashirin da bakwai-bakwai.

Wannan na nuna cewa tana bukatar ta dara su da maki idan tana son ta fice daga rukunin kungiyoyin da ba za su tsira daga fadawa zuwa gasa ta kasa da Firimiya ba.

Irin halin da take cikin ne ya sa ya zama dole ta nemi yadda za ta samu maki a karawar da za ta yi da Arsenal.

Bugu da kari, maki uku kawai Southampton ta iya samu a karawa 15 da ta yi da kungiyoyin da ke sama-saman a gasar Firimiya.

Wannan shi ya sa wasu ke ganin kungiyar za ta sha kaye a gidan Arsenal.

Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce damar nasara a wasansu da Southampton da kuma lashe kofin gasar Firimiya na hannun kungiyarsa kuma kungiyar za ta yi amfani da damar/Photo:Reuters

Sai dai kuma wasu na ganin ba nan take ba domin kuwa kungiyoyi na iya ba da mamaki a gasar Firimiya.

Ba za mu yanke kauna ba

Kocin Southampton, Ruben Selles, yana cikin wadanda suke ganin kungiyar za ta iya sauya halin da take ciki a yanzu.

A lokacin da yake magana da manema labarai ranar Juma’a gabanin karawar kungiyarsa da Arsenal, Ruben Selles ya ce yana ganin kulob dinsa zai taka rawar gani a karawar.

“Ba ma nuna wata alama ta karaya. Mun san muna bukatar mu jajircewa da kuma cigaba da taka leda yadda ya kamata,” a cewarsa a lokacin da yake ganawa da manema labarai yana mai cewar kungiyar ba za ta yanke kauna ba.

Kocin Southampton, Ruben Selles, yan wasansa za su matsa wa 'yan Arsenal ahr sai sun samu damar zura kwallaye a ragar Arsernal kuma suka doke kungiyar dake saman teburin Firimiya/Photo:Reuters

“Za mu yi kokarin kasancewa cikin hayyacinmu, mu matsa musu kuma mu zura kwallo ragarsu, ” in ji Selles.

Ya kara da cewar kallon da yake yi wa kungiyar Arsenal kallon wata kungiya ce da shi yake son ya doke.

Bayan wannan wasan, Arsenal za ta kara ne da Man City wadda take neman ta kwace saman teburin daga gare ta a rabar Laraba.

TRT Afrika da abokan hulda