Victor Osimhen ba zai samu damar buga wa ƙasarsa Nijeriya wasa ba a gasar neman cancantar samun gurbi cin Kofin Duniya na 2026 da ƙasar za ta kara da Afirka ta Kudu da kuma Benin a watan gobe ba, a cewar sanarwar da Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ƙasar (NFF) ta fitar a ranar Talata.
Hukumar NFF ta ce ɗan wasan gaba na Napoli Osimhen ya ji rauni kuma zai yi jinyar akalla makwanni hudu.
Yanzu haka dai ɗan wasan baya na Enugu Rangers Kenneth Igboke ne ya maye gurbinsa.
Nijeriya za ta ƙarbi bakuncin Afirka ta Kudu a birnin Uyo a ranar 7 ga watan Yuni, sannan bayan kwana uku ta wuce zuwa Cote d'Ivoire domin buga wasa da ƙasar Benin don neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a 2026.
Matsin lamba
Tawagar Nijeriya dai na fuskantar matsin lamba don samun nasara a wasannin biyu da za ta fafata, yayin da a yanzu take matsayi na uku a rukunin C da maki biyu daga wasanni da dama da ta buga.
Afrika ta Kudu ce ta biyu a rukunin C da maki uku, yayin da Benin ke mataki na karshe da maki daya.
Rwanda ce ke kan gaba da maki hudu, yayin da Lesotho da Zimbabwe ke da maki biyu kowaccensu.