Raphael Varane ya ce ya sha buguwa a kai yayin wasa. / Hoto: Getty Images

Raphael Varane, ɗan wasan Manchester United, kuma tsohon ɗan wasan baya na tawagar Faransa ya yi kira da a kula da kare lafiyar 'yan wasa bayan da ya sha shiga haɗari a lokacin buga ƙwallo.

Varane ya faɗa wa wata jaridar Faransa ta L'Equipe ranar Talata cewa, "Idan muka duba wasannina uku mafi muni, akwai aƙalla guda biyu da na buga bayan na samu buguwa a kai 'yan kwanaki kafin wasan."

Ɗan wasan ya yi nuni da wasan da tawagar Jamus ta doke ta Faransa da ci 1-0 a zagayen kwata-fainal na gasar Kofin Duniya na 2014. Sai kuma wasan gasar Zakarun Turai da Manchester City ta doke Real Madrid da ci 2-1 a zagayen 'yan-16 a 2020.

'Yan kwanaki kafin wasan da Faransa ta buga da Jamus, Varane wanda ke da shekaru 30 yanzu, ya ce ƙwallo ta bugi gefen kansa a wasan da suka buga da Nijeriya a zagayen 'yan-16.

Yanayin ruɗewa

"Yayin fara zagaye na biyu na wasan, an bugo ƙwallo inda ta same ni a gefen kaina, kuma hakan ya sa na faɗa cikin ragar ɗaya ƙungiyar. A ƙarshe na kammala wasan kaina a ruɗe".

Varane ya ƙara da cewa, "Ma'aikatan kulob ɗinmu sun jinjina ko zan iya buga wasan gaba da za mu fuskanci Jamus. Na rasa kuzari, amma a ƙarshe na buga wasan ba kumari. Ban san ko mai zai faru ba da a ce ƙwallo ta sake bugun kaina.

"Idan ka san cewa yawan samun buguwa a kai zai iya hallakawa, dole ka gaya wa kanka cewa kana cikin haɗari."

Varane ya bar buga ƙwallo a matakin ƙasarsa bayan da aka doke Faransa a wasan ƙarshe na gasar kofin Duniya ta 2022.

Ba a ganin alomomi

"A matsayinmu na 'yan ƙwallo da ke buga wasa a matakin ƙwararru, mun saba da bugu ko jin ciwo a wasa. Kusan kamar sojoji muke, muna da juriya, amma buguwa a kai abu ne da alamominsa suke a ɓoye.

Ya ƙara da cewa, "Muna buƙatar mu dinga magana game da haɗarin sake samun buguwa a kai ko maimaituwar buguwa, saboda amfani da kai wajen dukan ƙwallo".

Ya yi kira da a rage amfani da kai a ƙwallo lokacin atisaye don kaucewa haɗarin buguwa a kai.

Haɗarin bugu na biyu yana faruwa ne yayin da ƙwaƙwalwa ta kumbura cikin sauri kafin ta warke daga buguwar da ta faru a baya.

A Ingila, tsoffin 'yan wasa 10 da wasu iyalan 'yan wasa da suka mutu sakamakon buguwa a kai su bakwai sun shigar da hukumomin wasanni ƙara. Sun zarge su da cewa "da ma sun san da matsalar" haɗarin buguwar kai da lahanin ƙwaƙwalwa ga 'yan wasa amma ba su ɗauki matakin kare su ba.

TRT Afrika da abokan hulda