Uruguay ta kawo karshen wasanni 14 da zakarun gasar cin Kofin Duniya Argentina suka buga a jere ba tare da an doke su ba inda suka tashi da ci 2-0 a ranar Alhamis.
Argentina, wacce ta lashe Kofin Duniya a bara, ba ta yi rashin nasara ba tun bayan da Saudiyya ta lallasa ta da ci 2-1 a wasan farko da suka buga a gasar cin Kofin Duniya a bara a kasar Qatar.
"Tun daga lokcin ba mu sake jin dadi ba," a cewar Kyaftin din Argentina Lionel Messi.
"Rashin nasarar ta zama jarrabawa a gare mu, domin kungiya ce mai kwazo kuma fafatawa da su akwai wahala,'' in ji shi.
Messi ya kara da cewa, "Suna da gwarazan 'yan wasa tsayayyu a tsakiyar filin, ba mu samu hanyar kwace kwallon na tsawon lokaci ba."
Uruguay ce ta fara cin kwallo ta hannun dan wasan bayanta Ronald Araujo a minti na 41 da fara wasa, sannan dan wasan gaba na Liverpool Darwin Nunez ya samu nasarar cin kwallo a mintina 87, inda suka yi nasara a karshen wasan da aka buga a filin wasa na Bombonera da ke Buenos Aires.
Wannan ne karo na farko da Lionel Messi da Argentina suka sha kashi a neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026, kana rashin nasara ta farko tun bayan doke su da Saudiyya ta yi da ci 2-1 a wasan farko na gasar cin Kofin Duniya ta 2022 a Qatar.