A ranar Laraba da daddare ne aka kammala zagayen ‘yan-16 na gasar cin kofin Zakarun Turai, UEFA Champions League, inda ƙungiyoyi takwas suka tsallaka matakin kwata-fainal.
Zaƙaƙuran ƙungiyoyin sun fito ne daga ƙasashen Turai huɗu kacal, inda Sifaniya ke kan gaba da ƙungiyoyi uku, sai Jamus da Ingila masu ƙungiyoyi biyu-biyu, sai kuma Faransa mai ƙungiya ɗaya.
Ƙungiyoyin su ne Real Madrid, Barcelona, da Atletico Madrid daga Sifaniya, sai Bayern Munich da Borussia Dortmund daga Jamus, sai Manchester City da Arsenal daga Ingila, sai kuma Paris Saint-Germain daga Faransa.
Fitar da jadawalin wasanni
A ranar Juma’a 15 ga Maris da ƙarfe 11 na safe agogon GMT za a gudanar da canke don fitar da jadawalin wasannin matakin kusa da na ƙarshe, inda kowane kulob zai san abokin karawarsa.
Za a yi taron tsara jadawalin ne a hedkwatar hukumar UEFA a birnin Nyon na Switzerland. Sai dai ba jadawalin zagaye na gaba kawai za a fitar ba, har da na wasannin dab da na ƙarshe.
A taron na Juma’a za a fayyace guraben da kowace ƙungiyar da ta yi nasara a kowane rukuni za ta samu kanta, don gane da wa za ta iya haɗuwa a gaba.
Hakan ne zai sa a iya hasashen ƙungiyar da kowane kulob zai iya haɗuwa da ita, kafin ya isa ga wasan ƙarshe wanda za a buga a filin wasa na Wembley da ke birnin Landan na Ingila.
A wannan karo, canken zai zama buɗaɗɗe, wato ƙungiyoyin da suka fito daga ƙasa ɗaya za su iya fuskantar junansa a wasa.
Za a fara buga zagayen farko na wasannin kwata-fainal ne a ranakun 9 da 10 na Afrilu, sai zagaye na biyu a ranakun 16 da 17 na Afrilun.
Sai zagayen farko na wasannin dab da na ƙarshe a ranar 30 ga Afrilu, da 1 ga Mayu, sannan a buga zagaye na biyu a ranakun 7 da 8 ga Mayu.
Za a buga wasan ƙarshe ne ranar 1 ga watan Yuni a birnin Landan.