An kafa Beşiktaş tun shekara 121 da suka wuce kuma babban filin wasanta yana birnin istanbul na Turkiyya. / Hoto: AA

Wasa na huɗu a kakar Europa ta bana da za a buga ranar 28 ga Nuwamba tsakanin ƙungiyar Beşiktaş ta Turkiyya da Maccabi Tel Aviv ta Isra'ila, ya samu sauyin wajen da za a buga shi, sakamakon rashin jituwa tsakanin Turkiyya da Isra'ila.

Ƙungiyar Beşiktaş ta Turkiyya ta sanar da cewa an dakatar da buga wasan a cikin Turkiyya, inda a yanzu za a nemi wata ƙasa ta daban domin buga shi.

Sanarwar ta ce "Duba da yiwuwar samun tashin tashina, mahukuntan tsaron ƙasarmu sun yanke cewa za a buga wasan a wata ƙasa ta daban", ba a Istanbul ba inda nan ne filin wasan Besiktas yake.

Haka nan sanarwar ta bayyana cewa an samu tuntuɓa yadda ta dace tare da hukumar UEFA, sannan an samu izinin ɗauke wasan daga Tüpraş Stadium, sansanin Besiktas.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙungiyar da kuma UEFA, kan ƙasar da za a kai wasan, yayin da Besiktas ta bai wa masoyanta da ke Turkiyya haƙuri kan wannan sauyi.

Dangantaka tsakanin Turkiyya da Isra'ila ta yi tsami sakamakon mummunan yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda ya halaka fiye da mutane 40,000 da jikkata sama da 100,000; da kuma a Lebanon, inda Isra'ila ta kashe mutane sama da 3,000 tun Oktoban bara.

AA