Tsohon kocin Chelsea, Thomas Tuchel, zai bar Bayern Munich shekara ɗaya kafin kwantiraginsa ya ƙare bayan ƙungiyar ta sha kashi sau uku a jere lamarin da ya sa ake hasashen cewa za ta ƙare kakar bana ba tare da ɗaukar kofi ko ɗaya ba.
Bayern ta ce an yanke shawarar sallamar Tuchel ne bayan ya tattauna da shugaban ƙungiyar Jan-Christian Dreesen. Kwantaragin Tuchel za ta ƙare a kakar wasa ta 2024-25.
“A tattaunawar ƙeƙe-da-ƙeƙe da aka yi, mun yanke shawarar kawo ƙarshen alaƙarmu ta aiki a bazara bisa yarjejeniyar da duka ɓangarorin muka amince da ita," a cewar wata sanarwar da ƙungiyar ta ambato Dreesen yana bayyanawa.
“Babban burinmu shi ne mu samu sabon tsarin ƙwallon ƙafa wanda sabon koci zai jagoranta a kakar 2024-25.”
Kocin ne ya jagoranci Bayern a nasarar lashe kofin Bundesliga a kakar bara bayan ya karɓi ragarmar gudanar da ita a bazara, amma a halin yanzu ƙungiyar tana bayan Bayern Leverkusen da maki takwas.