Da kyar Arsenal, da ke saman teburin Firimiya, ta iya rike Southampton a wasan da suka yi a ranar Juma'a da daddare inda suka tashi da ci 3-3.
Tun da aka murza leda Southampton ta nuna tana son ta doke Arsenal ganin yadda ta zura kwallo uku a ragar Arsenal yayin ta take da ci daya.
Har zuwa minti 86 Southampton tana da ci uku ne yayin da Arsenal ke da ci daya.
Sai dai cikin minti huɗu Arsenal ta farke kwallaye biyu.
Odegaard ya zura wa Arsenal kwallo a minti 88, yayin da Saka ya zura mata ɗaya kwallon a minti 90.
Sakamakon wasan na nufin Arsenal tana gaban Manchester City, wadda ke neman kwace saman teburin Firimiya daga hannunta, da maki biyar kacal bayan ta sake zubar da maki biyu .
Tun da City tana da dakon wasa biyu, za ta iya shan gaban Arsenal idan ta iya nasara a wasannin da suka rage mata.
Sai dai kuma kocin Arsenal Mikel Arteta ya sha alwashin doke City a gida a karawar da za su yi a Etihad ranar Laraba.
Tun shekarar 2015 dai Man City ba ta sha kaye a gida a hannun Arsenal ba.
Amma a jawabin da ya yi bayan sun sha da kyar a hannun Southampton, Arteta ya ce " wannan wani mawuyacin lokaci ne. Lokaci ne da ya kamata mu hada kanmu har zuwa karshe.
Muna da abubuwa da dama da muke bukatar yi a wannan kakar. Gasar ba ta kare ba. Kawo yanzu muna gaba da maki biyar. ".
Bayan Arsenal ta barar da maki shida a wasanni ukun da ta yi kwanan nan, babu tabbacin cewa za ta iya nasara a wasanni shidan da suka rage mata a gasar Firimiyar bana.
Sai dai Arteta na ganin yaransa, wadanda suka fi na ko wacce kungiya kuruciya a gasar Firimiya kakar bana, za su yi iya kokarinsu a gidan City.
”Dole mu je mu yi nasara a can (Etihad)," in ji Arteta.
Ranar Laraba za a sani ko Arsenal za ta iya cika wannan burin na kocinta.