A ranar Laraba ne tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta kara da tawagar Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu, don tantance wa zai buga wasan karshe a gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka da ke gudana a kasar Ivory Coast.
Za a buga wasan ne a birnin Bouacke, gari na biyu mafi girma a kasar, inda duk kungiyar da ta samu nasara za ta sami gurbin buga wasan karshe na gasar ta AFCON.
Da yake zantawa da 'yan rahoto na hukumar CAF, kocin Nijeriya Jose Peseiro ya bayyana dogaronsa kan karfin masu tsaron gida na tawagar Super Eagles wadanda suke hana cin kwallo.
Peseiro ya ce, "Na gamsu da 'yan wasanmu amma ina kokarin ganin sun kara himma. A baya ba mu da wasu manyan 'yan wasa kamar Kelechi Iheanacho da Joe Aribo, shi ya sa abubuwa suka dan yi mana wahala."
A gasar ta AFCON, cikin wasanni hudu na karshe na duka tawagogin kasashen biyu, ba a zura kwallo a ragar mai tsaron gidans kowannensu ba. Hakan na nuna jajircewar kowace tawaga wajen tsaron gida.
Wannan ne ya sa ake kallon wasan da kasashen biyu za su yi ranar Laraba a matsayin zakaran gwajin dafi.
Peseiro ya nuna farin cikinsa kan yadda 'yan wasan baya na Super Eagles suke tare barazanar cin kwallo zuwa yanzu. Don haka ya shirya ganin 'yan wasansa na gaba sun dage wajen ciyo kwallo don su iya cin Bafana Bafana.
Nijeriya za ta dogara kan 'yan wasan tsakiya irin su Alex Iwobi da Zaidu Sanusi wajen kawo kwallo ga 'yan wasan gaba irinsu Moses Simon, da Ademola Lookman, da kuma babban tauraro Victor Osimhen.
A tarihin haduwar kasashen biyu, bayan karawa sau 14, tawagar Nijeriya ta samu galaba sau 7, sannan sun yi janjaras sau 5, sai kuma Afirka ta Kudu ta yi nasara sau 2 kacal.
A bangaren Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu, za su dogara kan mai tsaron raga Ronwen Williams domin tare harin zakarun 'yan wasan na Super Eagles.