Wannan ne karo na shida da wata kungiya daga Sifaniya ta fitar da Manchester United daga gasar Zakarun Turai. Hoto/Getty              

Sevilla ta fitar da Manchester United daga Gasar Europa bayan ta doke ta da ci 3-0 a wasa na biyu na zagayen dab da na kusa da karshe ranar Alhamis.

Sevilla ta zura kwallon farko ne ta hannun Youseff En-Nesyri minti takwas kacal da soma wasa, yayin da Lucas Ocampos ya jefa kwallo ta biyu, ko da yake alkalin wasa bai yarda da ita ba.

Daga bisani Loic Bade ya cilla kwallo a ragar United, sannan En-Nesyri ya maka kwallo ta uku a ragar United.

David de Gea ya gaza tare kwallo ko da guda daya, sai kuma Harry Maguire da bai tabuka komai a wasan ba.

Sevilla za ta fafata da Juventus a zagayen dab da na karshe ranar 11 da kuma 18 ga watan Mayu.

Wannan ne karo na shida da wata kungiya daga Sifaniya ta fitar da Manchester United daga gasar Zakarun Turai.