Sabon kocin Beşiktaş Ole Gunnar Solskjaer ya yi bayani ga 'yan jarida gabanin wasan da ƙungiyar za ta kara da Athletic Bilbao ranar Laraba a gasar UEFA Europa League.
Solskjaer ya karɓi aiki a ƙungiyar a makon jiya, kuma ya tarar da Beşiktaş a mataki na 6 a teburin babbar gasar Super League ta Turkiyya, da maki 31, bayan buga wasanni 19.
Yayin jawabin nasa, Solskjaer ya ce, "Sauyin koci abu ne da ke nuna akwai wata matsala a ƙungiya.
Na ji daɗin zaman a Manchester United kuma wannan ya wuce. Ina fatan zamana a Beşiktaş zai yi kyau. Ɗorewata a nan tana da muhimmanci.
"Zan ba da duka ƙwazona ga Beşiktaş, zan yi iya ƙoƙarina a matsayina na mutum da kuma matsayina na koci.
"Na san wasanmu da Bilbao zai yi zafi saboda sun doke Fenerbahçe. Mu dai mun shirya kuma ina fatan wasan zai mana kyau."
Kocin ya ƙara da cewa duk sabon koci ya kan ƙara ƙaimi ga ƙungiya, kuma ba abin mamaki ba ne wasu 'yan wasa sun yi tararrabi.
Ɗabi'ar atisaye
Da yake ƙarin haske kan ingancin ƙungiyar, Solskjaer ya ce yana fatan kafa ɗabi'ar atisaye don samad da 'yan wasa maus iya ƙwato nama daga bakin kura, yayin da suke taimakon junansu. Muna da haziƙan 'yan wasa.
Ya kuma ƙara da cewa babbar manufarsa ita ce makomar Beşiktaş inda zai mai da hankali kan hakan sannu a hankali. Abin da na gani zuwa yanzu ya ba ni ƙwarin gwiwa duk da ba daɗewa na yi ba.
Sai dai ya yi nuni da cewa akwai masu tsaron baya da dama da suke jinya a halin yanzu. Amma ya ce zai yana da shirin da ya tanada a zuciyarsa.
Ya kuma ce yana fatan gina ƙungiya mai aiki tuƙuru wadda 'yan wasanta ke yaƙi da gudu iya ƙarfinsu. Sannan ya ce bai taɓa horar da ƙungiyar da ke aiki da nawa ba a rayuwarsa.