Tsohon zakaran wasan dambe na Afirka ta Kudu a duniya Dingaan Thobela ya rasu yana mai shekaru 57 a duniya.
'Rose of Soweto' ya mamaye dukka manyan sassan wassanin dambe na duniya bayan da ya lashen lambar yabo ta Hukumar Dambe ta Duniya (WBO), da na Kungiyar dambe ta Duniya (WBA) da kuma Majalisar Dambe ta Duniya (WBC) a sana'ar da ya soma tun daga shekarar 1986 har zuwa 2006.
An tsinci gawarsa a gidansa da ke birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu bayan rashin lafiya da ya yi fama da shi, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito.
"Thobela ya kasance gwarzon ɗan wasa wanɗa mamaye zukata da ruhin al'ummar Afrika ta Kudu,'' a cewar sanawar Ministan wasannin kasar Zizi Kodwa.
"Muna jimamin rashin ɗan wasan da ya yi matukar kokari wajen daukaka fannin wasannin Afirka ta Kudu ta hanyar nasarar da ya samu a wasan damɓen 'boxing', in ji shi.
Muhimman kyautukan da ya samu waɗanda suka kara sa ya fi fice sun haɗa da nasarar da ya samu kan Tony Lopez inda ya samu lambar yabo ta WBA 'lightweight title' da kuma karawar da ya yi da Glenn Catley da ya kai shi ga samun lambar yabo ta WBC 'super-middleweight title'.
Dan damben boksin dan kasar Afrika ta Kudu Kevin Lerena ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Ba za a taba mantawa da hazaka da jajircewarka a filin daga ba.
"A Ko yaushe kana bani goyon baya tare da yarda da iyawata, da kuma karfafa min don na iya kaiwa gashi . Na gode da ƙwarin gwiwarka," in ji sakon Kevin.