Cristiano Ronaldo zai ci gaba da zama a cikin tawagar 'yan wasan Portugal a wasannin da za su kara da Croatia da Scotland a wata mai kamawa a gasar cin kofin nahiyar Turai duk da rashin nasarar ƙungiyar a gasar Euro ta 2024.
Ɗan wasan mai shekaru 39 ya gaza cin ƙwallo a tawagarsa a yayin da ya ƙara tarihi a cin kofin gasar nahiyar Turai karo na shida, inda aka yi waje da ƙungiyar a wasan kusa da na ƙarshe, amma ya ci gaba da samun goyon bayan koci Roberto Martinez.
''A lokacin da zan bar tawagar ƙasar, ba zan gaya wa kowa ba... A halin yanzu abin da nake so na yi shi ne na taimaka wa tawagata,'' in ji Ronaldo a wata hira da gidan talabijin na Portugal ya yi da shi a farkon makon nan.
Wasu daga cikin tawagar
Ronaldo dai ya fara sabuwar kakar bana ne da cin ƙwallaye huɗu a wasanni da dama da ya bugawa ƙungiyar Al-Nassr ta ƙasar Saudiyya kuma da alama zai ci gaba da jagorantar fafatawar da Portugal za ta yi, inda ɗan wasan gaba na Paris Saint -Germain Goncalo Ramos a ƙungiyar ya samu rauni a idon sawunsa.
Yayin da tsohon ɗan wasan baya na ƙungiyar, Pepe ya sanar da yin ritaya daga wasan ƙwallon kafa yana mai shekaru 41 a farkon wannan watan.
A ɗaya bangaren kuma Kocin ƙungiyar Martinez yana sa rai a wasan ranar Juma'a wajen kiran ɗan wasan gefe na Sporting Geovany Quenda mai shekaru 17.
Ɗan wasan baya na Chelsea Renato Veiga da mai tsaron baya Lille Tiago Santos suna daga cikin sabbin fuskoki a cikin tawagar 'yan wasan Portugal da za su fafata da Croatia da Scotland a ranar 5 da 8 ga watan Satumba a Lisbon.