Shafin labarun wasanni na ESPN UK ya wallafa a X cewa mashahurin ɗan wasan ƙwallo ɗan asalin Portugal, Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin samun adadin mabiya miliyan guda cikin awa ɗaya da rabi a shafin YouTube.
Ronaldo wanda ke buga wasa a ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta cewa ya buɗe shafi a kafar YouTube, inda ya sanya mahaɗin da za a dannan a duba shafin.
Awa ɗaya da rabi bayan wallafa saƙon nasa, shafin YouTube ɗin mai suna @Cristiano ya samu mabiya miliyan ɗaya da 'yan kai.
Yayin da sanarwar Ronaldo take cika awa huɗu da wallafawa, tuni shafin ya cika mabiya har miliyan huɗu.
Da ma dai an daɗe ana dakon Ronaldo ya buɗe sahihin shafin Youtube, ganin cewa yana da miliyoyin mabiya a sauran shafukansa, kamar na Instagram da Twitter.
Tsawon shekaru Cristiano Ronaldo shi ne ya fi kowa mabiya a shafin Instagram.
An sha ƙirga Cristiano Ronaldo cikin mafi shahara a kafafen sadarwa a duniya, inda rahotanni ke cewa yana samun miliyoyin kuɗin talla, saboda duk abin da ya wallafa yakan samu kulawa daga mabiyansa cikin ƙanƙanin lokaci.