An ga sunan gwarzon ɗan ƙwallon duniya mai riƙe da kambin Ballon d'Or, wato Rodri, cikin jerin sunayen 'yan wasan da Manchester City ta gabatar don su buga mata wasan da za su yi da Real Madrid ranar Talata mai zuwa.
Ganin sunan Rodri ya ba da mamaki saboda yana jinya, kuma ba a ga sunan Victor Reis ba, wanda shi ne sabon ɗan wasan da City ta sayo kan fam miliyan £29.5 a kakar cinikin 'yan wasa da aka rufe a farkon satin nan.
Reis dai shi ne ɗan wasan da aka yi tunanin an sayo shi don maye gurbin Rodri da ya daɗe yana jinya, kuma wanda ake ganin rashinsa na daga cikin dalilan da suka janyo wa Man CIty koma-baya.
Ɗan asalin Sifaniya mai shekaru 28, Rodri ya samu babban rauni a gwiwarsa tun a wani wasa da City ta kara da Arsenal a Satumban bara, inda ya tsinka jijiyar bayan gwiwarsa wadda har sai da aka masa tiyata.
A baya rahotanni sun ce Rodri ba zai sake iya buga wasa ba har zuwa ƙarshen kakar bana. Sai dai haziƙin ɗan wasan ya yi ta ƙoƙarin farfaɗowa, inda yake bayyana burinsa na dawowa filin wasa da wuri.
Hamayya da Real Madrid
A cewar mujallar The Independent, duk da cewa Rodri yana farfaɗowa daga jinya, kocin Man CIty, Pep Guardiola ya zaɓi saka shi a tawagar da za su buga wasa mai muhimmanci na gasar Zakarun Turai.
Manchester City ta samu damar buga wasan share-fage bayan sha da ƙyar a zagayen rukuni inda ta samu doke Club Brugge a wasan ƙarshe na matakin.
Sai dai wasan zai kasance mai zafi saboda za su haɗu da Real Madrid ne, wadda ita ce ke riƙe da kofin, kuma sun sha haɗuwa a gasar ta Turai a 'yan shekarun nan har ana ganin sun zama 'yan hamayyar juna.
Dokokin hukumar UEFA sun amince wa ƙungiya ta sako ƙarin 'yan wasa uku a ɓangare na biyu da gasar Zakarun Turai a kakar wasa.
Sai dai City ta fuskanci ƙalubale, saboda sa sayo 'yan wasa har huɗu a Janairun nan kan jimillar kuɗin da ya kai fam miliyan £170.
Wannan ya sa Reis, ɗan wasan baya mai shekaru 19 da suka sayo daga Brazil ya rasa gurbi a jerin 'yan wasan da aka ƙaro, duk da cewa wani sabon ɗan wasan ɗan Uzbekistan, Abbosbek Khusanov ya samu waje.