Gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya a bana, Rodri, wanda ɗan asalin Sifaniya ne da ke buga wasa a Manchester City ya nemi ƙungiyar ta sayo abokinsa a tawagar Sifaniya, Nico Williams.
Rodri ya yi iƙirarin cewa Nico zai ji daɗin buga wasa a Man City sakamakon cewa yanayin garin Manchester ya yi kama da na garin da Nico yake wasa a halin yanzu.
Nico mai shekaru 22, yana taka leda a Athletic Bilbao ta Sifaniya kuma tana mataki na huɗu a taeburin LaLiga da maki 26 bayan wasanni 15.
Baya ga magana kan ɗauko abokinsa, Rodir ya yaba wa Nico kasancewar ya nuna bajinta a gasar Euro 2024 da tawagar Sifaniya ta lashe kofi, kuma yana nuna ƙwazo a ƙungiyarsa ta Athletic.
Rodri ya faɗa yayin wani bikin karramawa da jaridar AS ta shirya, sai dai Nico bai samu halartar taron ba saboda ƙungiyarsa na shirya wa wasan da za su buga da Real Madrid a maraicen Laraba.
Rodri ya ce, “A halin yanzu, zan so na kai shi zuwa [Manchester] City, ba na tababa, saboda zai ji sanyin Manchester, na san daidai yake da na garin Bilbao”.
Nico yana cikin zaratan matasan La Liga, kuma a bara ya ciyo wa Athletic ƙwallo 8 da tallafin ƙwallo 19 a wasanni 37. Sai dai a bana ƙwallo 2 ya ci da tallafin ƙwallo 5 a wasanni 18.
A yanzu hakan akwai maganganu da ke cewa manyan ƙungiyoyin Turai irin su Man City da Barcelona da PSG suna zawarcin Nico Williams.
Sai dai Nico ya sanya hannu kan tsawaita kwantirahinsa a Athletic a Disamban bara, har zuwa yunin 2027. Amma akwai saɗarar da ta ce za a iya sakin sa kan kuɗi dala miliyan $65, kuma adadin zai ragu bayan shekarar 2026.
Ana sa ran Nico zai taka rawar gani a wasan Athletic da Real Madrid, inda ƙwazonsa zai ƙara masa farin jini wajen ƙungiyoyin da ke fatan farauto shi.