Real Madrid, wadda sau ɗaya aka doke ta a kakar bana, tana da tazarar maki 13 da mai biye da ita wato Girona yayin da Barcelona ta koma ta uku inda take da sauran wasanni huɗu . / Hoto: Reuters

Real Madrid ta lashe kofin La Liga karo na 36 bayan Girona ta doke Barcelona da ci 4-2 a fafatawar da suka yi ranar Asabar a Estadi Montilivi.

Real Madrid, wadda sau ɗaya aka doke ta a kakar bana, tana da tazarar maki 13 da mai biye da ita wato Girona yayin da Barcelona ta koma ta uku inda take da sauran wasanni huɗu.

Ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jagoranta ta buge Cadiz da 3-0 a karawar da suka yi ta mako na 34 a filin wasa na Santiago Bernabeu.

An kwashe minti 45 na farko ba a zura ƙwallo ba, amma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Real ta ci ƙwallayen uku.

Brahim Diaz ya soma cin ƙwallo, sannan Jude Bellingham ya ci ta biyu yayin da Joselu ya zura ƙwallo ta uku a ragar Cadiz.

Nasarar ta Madrid ta bai wa Girona damar samun gurbi a Gasar Turai mai zuwa a karon farko.

Wannan shi ne kofin La Liga na biyu da Ancelotti ya ɗauka a Real Madrid bayan wanda ya lashe a kakar 2021/22.

TRT Afrika