Pep Guardiola ya yanke hukuncin cewa ba zai taɓa komawa tsohon kulob ɗinsa na Barcelona ba, bayan da ake ganin yana dab da barin kulob ɗinsa na yanzu, Manchester City.
Guardiola ya ce "ƙofa a rufe take", inda yake tabbatar da cewa ba zai koma Barca ba, kulob ɗin da ya jagoranta daga shekarar 2008 zuwa 2012.
Wannan na zuwa ne duk da cewa a baya Guardiola ya taɓa cewa a shirye yake ya koma filin wasa na Camp Nou, ko da kuwa a kyauta ne.
Tun a shekarar 2012 Guardiola ya bar Barca inda ya ɗauki hutu daga aikin horar da wata ƙungiya.
Daga nan ne ya karɓi aiki a Bayern Munich ta Jamus, sannan daga bisani ya taho Manchester City, inda a yanzu yake tun shekara ta 2016.
Da yake magana a wani shiri na 'yan jaridu na Legends Trophy, an tambayi Guardiola ko ƙofar komawa Barcelona ba a buɗe take ba, amma sai ya amsa da cewa: "E, a rufe take."
A City, Guardiola ya jagoranci City wajen lashe kofin gasar Firimiya a karo na huɗu a jere, inda ake ganin suna da burin kafa sabon tarihin cin kofin gasar a karo na biyar a jere, a baɗi.