A yanzu Onana yana ganin cewa yana kara samun cigaba a ingancin wasansa. / Hoto: Reuters / Hoto: AFP

Golan Manchester United, Andre Onana ya ce lokacin shanawarsa na nan zuwa, bayan da a yanzu yake ta fafutuka domin bai saba da rayuwa a Birtaniya ba, yana mai cewa komai baƙo ne a wajensa.

Onana yana ganin a yanzu ya sauya salon wasansa bayan shawo kan 'mawuyacin lokaci' a watannin farko na zuwansa Manchester United.

Ɗan wasan wanda ɗan asalin Kamaru ne ya je kulob ɗin ne daga Inter Milan a watan Yuli, kan fam miliyan 47.2 (dala miliyan 60). Sai dai jerin kurakurai a wasansa sun janyo zura masa tarin ƙwallaye.

Onana, ɗan shekara 27, ya bayyana yadda sabawa da rayuwa a ƙasar Birtaniya ta yi masa wahala da fari.

Ya ce, "Na shafe watanni shida ko bakwai ba na iya wasa da kyau, ko jin ɗadin kaina".

"Abin ya min wahala amma yanzu ina jin sauƙin lamura saboda komai sabo ne a wajena. Na sha wahala kafin na fara jin daidai saboda dalilai da dama, kasancewar na zo wata baƙuwar ƙasa.

'Zan shana a gaba'

Onana ya ƙara da cewa, "Amma a yanzu komai ya yi daidai. Ba na son yin magana kan ƙoƙarina saboda na san wane irin mai tsaron raga ne ni, kuma na yi ƙoƙari a baya."

"Don haka a wajena abu mafi muhimmanci shi ne na zama cikin shiri, na samu farin ciki, kuma na shana."

Gabanin wasansu da Manchester City ranar Lahadi, Onana ya bayyana ƙalubalen da ya fuskanta lokacin fara rayuwarsa a Birtaniya.

Kurakuran mai tsaron ragar a wasannin United na gasar Zakarun Turai sun janyo wa kulob din asara, amma kokarinsa ya karu sosai kuma yana da yakinin cewa yana kara samun cigaba a ingancin wasansa.

Lokacin sauyi

Ya ce "Ina ganin cewa ina samun sauyi a wasana amma a filin wasa ina bukatar natsuwa saboda komai ya canja min".

"Tabbas a kakar bara na koma Milan daga Ajax, amma hakan bai min wahala ba."

"Amma ya dauke ni watanni bakwai zuwa takwas a nan. Lokaci ne da na kwashe ina nakaltar abubuwa, wasa bayan wasa. Ina fatan za mu yi nasara a karshe."

Onana ya ce ya samu goyon baya daga abokan wasansa tun lokacin da ya zo Old Trafford.

Ya ce, "A kullum suna da yaƙini kan ƙoƙarina, tun da fari suna ce min 'Andre, saurara ka ji, ka iya wasa, lokaci ne kawai zai nuna'".

Na yi gaba

"Ina farin ciki sosai, musamman saboda goyon bayan da na samu, da kuma masoyana. Suna nuna min kirki a kowane lokaci, ina musu godiya."

"Ina ganin komai ya wuce yanzu. Yanzu lokacin neman nasara ne kuma ina ganin murnarmu tana nan zuwa a gaba."

TRT Afrika