An ƙiyasta Manchester United za ta samu kuɗn-shiga da ya kai fam miliyan £680 (dala miliyan $873). / Hoto: Reuters

Hukumomin Manchester United na shirin gina ƙayataccen filin wasa bayan sun rushe shahararren filin wasa na Old Trafford.

Hamshaƙin attajiri Sir Jim Ratcliffe wanda yake jagorantar mamallaka kulob ɗin tun watan Fabrairu, da kamfaninsa na INEOS suna hanzarin sake fasalin ƙungiyar.

Bayan naɗa sabon shugaban gudanarwa, da daraktan wasanni, da daraktan fasaha, da kuma kwaskwarima a filin atisaye, ya kuma ci gaba da neman hanyoyin inganta kulob ɗin.

Sai dai babban matakin gyara ƙungiyar zai zo nan gaba, wato rushe Old Trafford da maye gurbinsa da sabon filin wasa mai ɗaukar mutane 100,000.

Ana sa ran sabon ginin zai ci wa ƙungiyar Fam biliyan biyu (dala biliyan 2.5), inda masu sharhi suke cewa Ratcliffe da kulob ɗin su zuba kuɗinsa, maimakon amfani da kuɗin gwamnati.

Tun bayan kammala sayan hannun jari kashi 27 cikin 100 na kulob ɗin, Ratcliffe ya fara maganar sake gina Old Trafford, inda ya kafa kwamitin duba hanyar da ta fi dacewa a bi.

Hukuncin kwamiti

Kwamitin na ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban tawagar Ingila ta London 2012 Olympics, Sebastian Coe, sannan akwai mambobi kamar Gary Neville da Magajin garin Manchester, Andy Burnham.

A ƙarshe, kwamitin ya yanke hukuncin cewa gina sabon filin wasa shi ne mafi a'ala. Cikin manyan dalilan hakan akwai cewa filin bai kai na sauran manyan ƙungiyoyi ba, kamar Manchester City, Arsenal, Liverpool da Tottenham.

Filin na Old Trafford ya tsufa kuma yana fama da matsalar kayayyakin sadarwa, da ƙanƙantar allon nuna sakamako, da rashin manyan sikirin na nuna bidiyon wasa.

Sannan hanya tsakanin kujeru ta tsuke inda take haifar da cikowa yayin fara wasa da lokacin hutun rabin lokaci da lokacin tashi. Kuma kujerun filin sun yi kusa da kusa.

Yoyon ruwa

Akwai kuma matsalar yoyon ruwa da aka gani yayin wani mamakon ruwan sama da aka yi a wasan Man United da Arsenal na bara, wanda ya jiƙa magoya bayan kulob ɗin, kuma ya mamaye ɗakin canja kaya.

Wannan ne ya sa aka lasafta cewa aƙalla gyaran filin wasan na buƙatar fam biliyan £1.1 (dala biliyan $1.4), kusan rabin kuɗin gina sabon filin wasa. Ga kuma matsalar yin gini a kewayen layin dogo.

Haka kuma, akwai wani yankin ginin Old Trafford wanda yana nan yadda yake tun ginin farko na 1909, duk da fuskantar harin yaƙin duniya na biyu. Shi ya sa ƙwararru ke ganin kayan da aka gina filin suna buƙatar sauyawa don sun tsufa.

Gina sabon filin wasan zai ba da damar faɗaɗa shi ya iya ɗaukar mutane har 100,000, wanda zai ishi buƙatun masu son tikiti.

A yanzu Man United tana da tarin mambobi masu biyan kuɗin rajista da suka kai 330,000, sama da duk wata ƙungiyar ƙwallo a duniya, inda kuma take da mutum 120,000 da ke jiran sayen tikitin kakar bana.

TRT Afrika