Ɗan wasan gaba na Chelsea, Nicolas Jackson ya sha alwashin ci gaba da taka leda a ƙungiyar, inda ya rattaba hannu kan sabuwar kwantiragin da zai ci gaba da buga wasa a Stamford Bridge har zuwa 2033.
Jackson wanda ya zo Chelsea daga Villarreal a 2023, ya ƙara tsawon kwantiraginsa da shekara biyu, wato daga shekara takwas zuga shekara 10.
A kakarsa ta farko, Jackson ya ciyo wa Chelsea ƙwallaye 17 a duka wasannin da ya buga, ciki har da ƙwallaye 14 da ya ci a Gasar Firimiya. Yana kan gaba wajen gina ƙarfin 'yan wasan gaba da Chelsea ke da shi, inda yake ci da bayar da tallafin ƙwallo.
Ana sa ran Jackson zai ci gaba da kasancewa babban abin dogaro ƙarƙashin sabon koci Enzo Maresca. A kakar bana ya ci ƙwallaye biyu, ciki har da ƙwallo ɗaya a wasansu da Crystal Palace.
Maresca ya bayyana gamsuwarsa da yadda Jackson ke taka leda kuma ya tabbatar da tsawaita kwantiragin.
Duk da ana cewa Chelsea na neman ƙarin 'yan wasan gaba, a yanzu dai ta jaddada alaƙarta da Nicolas Jackson ta hanyar tsawaita kwantiragin nasa.